MUTANEN DA KE RAYUWA TARE DA KADOJI

0

MUTANEN DA KE RAYUWA TARE DA KADOJI

Daga Bishir suleman

Bishir Suleiman
Jaridar Taskar Labarai

Rayuwa wuri ɗaya tsakani Kadoji da Mutane a Gulbin Ƙasar Burkina Faso

Duk da kasantuwar Kada na daga cikin dabbobi masu saurin kisa a wajen farauta, amma a ƙasar Burkina Faso dake a cikin ƙasashen yammaci Afirika, abin ya sha bamban domin kuwa irin dangogin Kadoji ba su zama barazana ga al’umar wani yanki na ƙasar.

Domin kuwa a ƙauyen Bazoule dake da nisan kilomita Talatin daga babba birnin ƙasar wato, Ouagadougou, mutanan ƙauyen nayin ninkaya a gulbi ɗaya tare da ɗararuwan Kadojin lami lafiya sama da shekaru da dama.

Duk da irin mugun dafin dake akwai a haƙuran Kadojin, amma bai tsorata al’ummar ƙauyen balle har ya hana su ninkaya tare a cikin ruwan da kadaojin ke rayuwa.

See also  NIGERIA IS SET TO COMMENCE THE MANUFACTURE OF IRRIGATION EQUIPMENT!

Kamar yadda ake labartawa akwai daɗaɗɗar dangantaka tsakanin mutanan ƙauyen da waɗannan Kadoji tun a wajajen ƙarni na sha biyar. Sai da a yanzu mutanan ƙauyen na fama da tsananin fari wanda har ta kai ga matan kadojin suna boyewa dan babu gulben nikayar, wanda hakan ba ƙaramin jifa mutan cikin shiryawa nikayar ya yi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here