Manoma 225,000 Sun Sami Tagomashin Harkokin Noma A Shirin NIRSAL

0

A ci gaba da shirye-shiryensa na bunkasa harkokin noma zuwa ga talakawa, hadadden shirin na bayar da tagomashi da lamuni game da harkokin noma mai suna ‘Nigeria Incentibe-Based haring System of Agirculture,’ NIRSAL, ya kammala tsare-tsaren bayar da tallafi ga manoma akalla 225,000 na kasar nan, a karkashin shirin nan na babban bankin Nijeriya na Bunkasa Harkokin Noma, wato ‘Anchor Borrowers Scheme.’

Shirin ya tabbatar da samun cibiyoyi a kowace jiha a kasar nan, domin tabbatar da manoman daga ko’ina sun sami damar shiga sahun shirin. Hakan dai na daga cikin tsarin da babban bankin na Nijeriya ya bayar ga cibiyar NIRSAL domin tabbatar da yi wa manoma lamuni da saukaka harkokin noma a fadin kasar.

Wata takarda da ke dauke da sa hannun shugaban shirin na NIRSAL Alhaji Aliyu Abbati Abdulhameed, ta bayyana cewa akalla manoma kimamin 5,000 daga sassa 37 a jihohi 36 na kasar gami da babban birnin tarayya Abuja ne za su amfana da wannan tsarin kai tsaye.

A yayin da yake karin haske game da shirin, shugaban na NIRSAL ya ce hukumarsa ta ba wa kwamiti na musamman da ai sa idanu, mai suna PMRO ne zai tabbatar shirin ya kai ko’ina a fadin kasar nan. Ya ce an kaddamar da kwamitin ne domin ya tabbatar ba a sami matsala a gudanarwar shirin ba.

See also  PRESIDENT BUHARI COMMISSIONS NIGERIA/CAMEROON JOINT BORDER POST AND BRIDGE, REITERATES NEED FOR NEIGBOURLINESS

“Dalilin ba wa kwamitin PMRO wannan amanar shi ne, domin su kasance idanunmu a wajen gudanar da shirin, wanda muradinmu shi ne kowane manomi ya samu damar shiga cikin shirin domin bunkasa harkokin noma a fadin kasarmu Nijeriya. Babban burinmu dai shi ne wannan lamunin ya kasance jigo ne wajen ci gaba da farfadowar harkokin noma a fadin Nijeriya, wanda dama babban bankin Nijeriya ya yi alkawarin zai shiga ya sa hannu don tallafawa manoman,” in ji Alhaji Abdulhameed.

A yayin da yake mayar da jawabi, shugaban kwamitin na PMRO, Dk. Steben Ogidan ya ce, kwamitinsa ya shirya tsaf wajen sanya idanun ganin cewa manoman ba su karkatar da lamunin da suka samu daga wannan shirin wajen gudanar da wasu harkoki daban ba. “Ina mai tabbatar da cewa yadda kwamitin nan nawa na PMRO ya sa idanu kan wadanda aka ba wa lamunin, zai yi wahala wani manomi ya karkatar da abin da aka ba shi don biyan wasu bukatunsa na daban. Don haka, a shirye muke mu tabbatar komai ya tafi yadda aka tsara, kuma kowane lungu da sako na kasar nan ya samu shiga shirin,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here