ME YA FARU NE. A ZIYARAR SHUGABAN KASA BUHARI KATSINA?

1

ME YA FARU NE. A ZIYARAR SHUGABAN KASA BUHARI KATSINA?
Daga wakilanmu..
A ranar jumma a 29/6/2018 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo ziyarar jaje da tausaya wa ga wadanda iska da ambaliyar Ruwa suka shafa a Katsina.
Ziyarar wadda aka shirya za a Tara Masa wakilan wadanda abin ya shafa a fadar Mai martaba sarkin Katsina..Domin ya gana dasu yayi masu jawabin tausayawa..
Tun kafin ranar gwamnatin Katsina da kuma jam iyyar APC sun ta yayata da kamfen jama a su fito Domin yiwa shugaban kasar tarya ta kasaita..an fitar da shela da kuma jawabai wadanda gwamnan Katsina yayi rokon a fito a yi taron Dango da tururuwa..ga wannan babban Bako.da ya zai zo jahar.
Wata majiya Mai tushe ta tabbatar Mana da cewa.gwamntin Katsina ta ofishin sakataren gwamnatin Katsina..ta Rika baiwa” duk kungiyar da zata kawo jama a wajen, taron tallafi.na kudin Abinci da na mota Don saukakawa wadanda zasu taho daga wasu wurare masu nisa. Mutum ya bar hidimar sa. Yazo ya Kamata ka tausaya Masa, da Koda na mota ne.da Abinci.kamar yadda wani ya tabbatar Mani.
Majiyarmu. ta tabbatar da cewa da yawa kungiyoyi sun amshi wannan tallafin dai yawan mutanen da suke Jin zasu iya kawowa..
Duk wata kungiya da ka ganta ta daga tuta ko wani alami ta amshi wannan tallafin inji yadda wata majiya ta tabbatar Mani.
Amma binciken da mukayi..shine wasu kungiyoyin da suka amshi kayan aikin sai sukayi nasu..Wanda ya rubuta. Zai tallafawa mutane dari sai ya cakare kudinsa Aljifu ya kawo . kanne da dangi da abokan arziki mutune goma
Binciken mu ya gano wata kungiyar Mai rajin goyon Bayan gwamnatin Buhari. Wanda shugabanta ya iske taron matasa yace a dauke. Su hoto cikin su..kawai ya watsa hoton a social media..yace wai wadanda ya kawo ne .daya daga cikin matasan da yaga hotonsa shine yayi wa wannan jaridar​ koke a rubuce..” kawai iske mu yayi sai ya bamu naira dari biyar biyar yace mu dau hoto kawai ..sai muka gani Facebook cewa wai mune yaranshi da ya kawo”
Binciken mu ya tabbatar da cewa.. wannan ya Sanya.. wannan shine ziyarar shugaban kasa da akayi Babu fitowar jama a .Don Masa lale maraba .sosai tunda ya Zama shugaban kasa.
Sam in ka cire Inda wasu mutane suka Dan tsaya ..Sam Babu jama a..ba Wanda ya damu da ziyarar ba wani shauki. Ba zumudi..kowa hidimar gabansa yake.
Ba kamar da ba..Wanda zaka ga duk hanyar da zai bi tayi cak..saboda jama a.
Wannan hatta fadar shugaban kasa ta lura da wannan.inda wani a cikin tawagar​ ya tabbatar wa marubucin nan cewa. ‘ akwai matsala..ya kuma bukace shi da yayi Masa sharhin matsalar ya tura masa ta email)
Mai waccar maganar.yace duk Inda muka je ba Haka muke gani ba..in Banda jahar biniwai…Wanda shi kuma gwamnatin jahar ta roki kar a fito Don kar a samu matsalar.
Wani kuma na kusa da gwamnatin yace an dogara da wasu kungiyoyi ne..su kuma wadannan kungiyoyi.sun Zama shagunan kasuwanci ne kawai.. a fitar da kudi da sunansu..a Basu rabi..a yanke rabi.su ma su wafci Kashi bakwai cikin goma su ce wai da Kashi uku za suyi aiki.
Yace an watsar da tsantsan Yan siyasa..wadanda suka San mutane suke tare da mutanen su….yace a gaba dole sai gwamnati ta sake zage Damtse..

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here