Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya Zama Jami’in Gudanarwa na Jami’ar Karatu Daga Gida (NOUN)
Daga Abdurrahman Aliyu
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zama ma’aikacin jami’an Karatu da ga gida ta Nijeriya, in da ya shiga ofis a yau talata 3/7/2018 a matsayin jami’in gudanarwa na Jami’ar da ke reshen Abekuta da ke Jihar Ogun.
Shugaban Jami’ar Farfesa Abdallah Uba Adamu ne ya ba shi takardar daukar aikin bayan ya kammala karatun digrinsa na uku a Jami’ar.
Shi dai wannan aiki na jami’in gudanarwa na Jami’ar aiki ne na wucin gadi da tsohon shugaban zai rika gudanarwa,
Olusegun Obasanjo shi ne mutum na farko da Jami’ar ta yaye a Digiri na uku bangaren addinin kiristanci.
Daraktan da ke kula da reshen Abekuta na Jami’ar Farfesa Ibrahim Salawu Wanda ya sheda shigar Obasanjo ofis ya bayyana farincikin sa da murna kan wanna matsayi da aka ba Tsohon Shugaban kasar, inda ya zagaya da shugaban a cikin makarantar tare da sauran ma’aikatan cikin Farin ciki da annashuwa.
Obasanjo ya nuna jin dadinsa kan wannan Mukami da aka ba shi kuma ya yi alkawarin yin aiki Tukuru domin kawo cigaba ga Jami’ar.
Sanarwa daga Ibrahim Sheme Darkatan yada labarai na Jami’ar NOUN.