Kwamishinan Ƴansandan jahar Katsina CP Mohammed Wakili fsi ya Bayyana Nasarorin da Rundunarsa ta samu.
Daga Bishir Suleiman
A ranar laraba 4/7/2018 Kwamishi nan ƴansanda na jahar Katsina ya kira taron manema labarai dan bayyana nasarorin da rundunar tasa ta samu.
Taron ya gudana ne a Hedikwatar rundunar, inda kwamishi nan ya bayyana jin daɗinsa ga mahartar taron, daga bisani kuma ya ci gaba da bayyana ko a kwanan nan sun samun nasarar damƙe wasu da ake zargi da aikata fashi da makami, a ranar 27 ga watan yuli da ya gabata, na shekarar da ake ciki, da misalin takwas saura kwata na dare, ƴansandan masu fatirin na yankin sabon gari katsina ne, suka samu kiran neman agaji gaugawa daga Hajiya Aisha Abdullahi “T” mazauniyar sabuwar unguwa a cikin garin katsina, inda take faɗar ƴan fashi sun afka gidanta har sun yi ma ta fashin mota Toyota Hilanda kirar 2003 mai lamba AX 597 KTS kalar ruwan toka.
Matakin gaugawa da ƴansadan suka ɗauka ne, ya basu nasarar samo motar a inda ta yi hatsari, a kan titin kusa da masallacin Juma’a na GRA dake cikin garin Katsina. Sun tarar da mai tukin motar, kuma ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da aikata fashin ya mutu, a sakamakon haɗarin, a binciken da suka gudanar kan shaidar da suka samu ne a wajen, ƴansanda suka binciko sauran ƴanfashi da suka arce, suka samu nasarar kamo Sanusi
Abdullahi, wanda aka fi sani da “SAGA” mai shekaru 22 da kuma Mansur
Abdullahi wanda ake kira da “WASHA” mai shekara 21a ranar 28/6/2018 dukkansu mazauna sabuwar unguwar a cikin garin katsina.
Haka kuma, jami’an ƴansandan sun damƙe Aliyu Salisu “ALIYOS” mai shekara 22 a matsayin mutum na uku da ake zargi da aikata fashin, inda suka kama shi tare da wata mota Honda jeep CRV mai lamba BE 788 NSR kalar tsanwa tare wayoyin tafi da gidanka guda biyu da ya sato, dukkansu mallakin Nasiru Lawal mazaunin unguwar gidaje masu saukin kuɗi na Dutsin safe, a gida mai lamba 11 a layin Sarkin Arewa.
Da Kwamishi nan ƴansandan ke nuna kayayyakin da aka kama ƴanfashin da su sun hada da: Bindigar wasan yara, Adduna guda biyu, Hom tiyata Rikoda, Tsabar kuɗi Naira dubu Biyar da naira Talatin da kuma wayoyin tafi da gidanka guda biyu, da motoci guda biyu ɗaya kirar Toyota Hilanda da Kuma Honda Jeep CRV, haɗi da Fitilar hannu guda biyu.