YADDA AKA TURA MASU TADA KAYAR BAYA SUKA SAMO HORO A KASAR ISRA’ILA

0

YADDA AKA TURA MASU TADA KAYAR BAYA SUKA SAMO HORO A KASAR ISRA’ILA

Daga Abdurrahman Aliyu

Hon. Ahmad Idris Maje Dan majalisar Tarayya da ga jahar Filato ya bayyana cewa, Isra’ila ce ta horar da Matasan Filato 300 Dabarun yaki.

Wani faifan mai minti biyu da sakin hamsin da bidiyo da ake yadawa a kafafen sada zumunta, wanda me nuna wani zaman majalisar wakilai ta tarayya, inda dan majalisa mai wakiltar Wase Ahmed Idris Maje ya bukaci majalisar kasa ta yi bincike game da kashe-kashen da kae a jihar Filato, wanda ya tabbatar da cewa akwai sa hannun wasu ‘yan siyasa a kashe-kashen.

A sakamakon wani bincike da majalisar ta gudanar inda ta gano cewa, akwai wasu matasa 300 da kasar Isra’ila ta horar da su.
Ya kuma zargi wasu manyan ‘yan siyasa da hannu a rikice rikicen da ke aukuwa a jihar Filato wanda ake saurin dora alhakinsa kan Fulani makiyaya.
Ya ce, akwai lokacin da aka kama wasu kwantainoni 3 da ake zargin suna dauke ne da makamai, kuma an gano wani kamfanine da ya fito daga Isra’ila, ke da alhakin shigo da su.

See also  President Buhari Commissions Phase One of federal government Housing Project in Gombe State.

Dan majalisa Idris Maje ya nanata bukatar matukar ana so a gano karshen rikice rikicen da ke damun jihar Filato sai an binciko hannun da Isra’ila da wasu ‘yan siyasar jihar suke da shi a wannan matsalar tsaro, in kuwa ba haka ba to za a jigaba da bugun jakki ne ana barin taiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here