Daya daga cikin jiga jigan da suka kafa APC Akida ya yi wa bangaren na akida tawaye..ya koma bangaren APC Masari.. majiyar mu ta tabbatar da cewa..Hon Abubakar Saddiq Yar Adua..yanzu Yana tare da Gwamnan Katsina Aminu Bello MasariUB
Binciken​ jaridar nan da ake bugawa a Bisa yanar gizo Mai suna TASKAR LABARAI tayi ta gano ..Hon Saddiq Yar Adua ..an kawo shi har gaban gwamnan Katsina..ya tuba Bisa laifuffukan da yake Jin yayiwa gwamnan da kuma gwamnatin APC ta jaha da ta tarayya…
Kuma gwamnan​ na Katsina ya yafe Masa . jaridar Taskar labarai tayi kokarin Jin ta Bakin Hon Saddiq Yar Adua Amma abin yaci tura..Amma jaridar na da tabbacin neman gafara wadda Saddiq Yar Adua yayi a wajen gwamna na Katsina daga majiyoyi masu karfin gaske.