ME KE FARUWA TSAKANIN HON ABUBAKAR SADDIQ YAR’ADUA DA GWAMNA MASARI?

0

ME KE FARUWA TSAKANIN HON ABUBAKAR SADDIQ YAR’ADUA DA GWAMNA MASARI?

Wani labari da Jaridar Taskar labarai ta buga na cewa Hon Abubakar Saddiq ya tuba ga gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari a kan rawar da ya taka a APC Akida.

Wasu bayanai da suka kara bayyana sun tabbata cewa maganar tuba da neman gafara babu ita kuma ba a yi ta ba.
A labarin da Taskar Labarai ta buga ta bayyana cewa, ta yi kokarin jin ta bakin bangaren Hon. Saddiq Yar’adua , amma abin yaci tura.

Bayan labarin ya fita jaridar ta samu magana da wasu da ke taka rawa na kokarin daidai ta tsakanin Hon. Saddiq da Masari wanda kuma suka kara samun haske cikin yadda abin ke faruwa.

Jaridar ta samu magana da wani Dan majalisar tarayya daga jihar Katsina, wanda yace shi ne ke safa da marwa a tsakani yaga cewa an samu dai dai to.

Dan majalisar wanda na kusa da gwamnan Katsina ne, kuma Yana cikin wadanda ke tare da Hon Saddiq a siyasance lokacin da ana tafiya a inuwa daya ta APC,
Ya fada wa jaridar nan cewa labarin yazo mana cewa an je taron APC akida, ana tattauna mafita da makomar bangaren sai aka ruwaito cewa, wasu na maganar a koma PDP wasu kuma na zancen a marawa Abubakar Ismail Isah Funtua baya, sai Saddiq a nashi gudummuwar yace, shi ba zai koma PDP ba, kuma bai zai koma bangaren Abubakar Ismail ba.
Yace shi yana Akida ne domin APC a Katsina su gyara kura-kuren da ake yi, a kuma daratta wadanda suka yi wa jam’iyya wahala, aka kuma Dade a tare dasu.

A taron Hon Saddiq yace, matsalar sa da gwamnan Katsina ta neman gyara ce, ba ta batanci ko fadan ganin baya ba.

Don haka shi baya komawa PDP kuma baya marawa wani dan takara da bai kai Masari baya ba.

Dan majalisar yace da naji wannan ni kuma sai na dage sai na dai-dai ta tsakanin su, yace, Saddiq Mai gida na ne, a siyasa Masari kuma uba ne, don haka na yi ma gwamnan Katsina magana ya kuma amince, sai na yi wa Saddiq magana, shi ma ya saurare ni.

Dan majalisar yace,
har rubuta rahoton nan ba ayi ganawar Ido da Ido da Masari da Saddiq ba. amma dai ana tattaunawa​ mai ma’ana. kuma ta na bada amsa mai kyau.

Yace shi ne a tsakani kuma babu In da Saddiq ya samu Masari yace a yafe masa ya tuba, Dan majalisar ya nuna fushinsa da bacin ransa akan labarin da yace yana iya dakile wannan yunkurin nasu na alheri wanda zai amfani siyasa da cigaban Katsina.

Wani na kusa da Hon Saddiq Wanda ake wa laqabi da Alhaji Musa Miloniya Kankia yace, babu laifin tuba ko neman gafara tsakanin Hon Saddiq da gwamna Masari, yace magana ce ta banbancin yadda za a gudanar da jam’iyya da kawo cigaba baki daya, yace ita ce kadai.

Hon Saddiq a matsayin shi na gogagge a kan fannoni daban-daban yana da yadda yake da shawarwarin da an bi su jam’iyya APC a Katsina za ta kara sauke nauyin ta ga al’umma da karin tagomashi.

Wani na kusa da gwamnan Katsina Wanda bai bukatar a ambaci sunansa yace, wasu na kusa da gwamnan na Katsina sune basu bukatar irinsu Saddiq su matso kusa saboda sun san in suna a ciki ana yi dasu to fadar su da babakerensu yazo karshe, kuma yanzu Al’umma za a sanya a gaba bason rai ba.
Yace mun sansu kuma muna fatan Allah yayi mana maganinsu.

A labarin da Taskar labarai ta buga In da korafi yake kawai shi ne maganar ganawa da neman tuba, wanda dukannin bangare biyu na Saddiq da kuma na Masari suka musanta cewa bai faru ba. Amma sun tabbatar da cewa ana kan hanyar sulhu da fahimtar juna da dawowa a tafi tare a Inuwar jam’iyyar APC bangaren Adams Oshimole.

Wata majiya tace za a ci gaba da tattaunawa a karshen wannan satin ko cikin sati mai kamawa, wanda daga ita an dinke ke nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here