Fiye da mutum miliyon 68 a duniya ke gudun hijira

0

Fiye da mutum miliyon 68 a duniya ke gudun hijira
Inji Sakataren MDD

Daga Zubairu Muhammad

Sakataren Majalisar dinkin duniya Mr Antonio Guterres ya bayyana haka a ranar yan gudun hijira ta duniya da yake jawabi yace; mezakayi idan har wani abu ya tilastamaka barin gidanka .
A yau fiye da mutum miliyon 68 a fadin duniya duk yan gudun hijira ne wadanda rikici dabam dabam ya rabasu da muhallinsu suka gudu domin niman mafaka a duniya.
Ya kara da cewa yawan alumman dake gudun hijira ya kai adadin mutanin wasu manyan qasashe a duniya.
Mr Antonio yace; a shekarar data gabata kididigan da akayi a duk sakon na agogo sai an samu yan gudun hijira a duniya. Masamman qasashe matalauta.
Saboda haka a wanan rana ta Yan gudun hijira ya zama dole mu canza tunaninmu ta yadda zamu taimaka masu .
Yace;ansar wanan magana zai farane ta hanyar hadin kanmu da basu goyon baya mai mahimmanci.

Yace;gaskiya wanan al’amari yana matukar damuna saboda zakaga Yan gudun hijira basasamun taimakon da yakamata ace sun samu.
Saboda haka babu bukatar ace munyiwa wanan ranar ta Yan gudun hijira gyarar fuska.
A wanan zamanin a fadin duniya babu wata alumma ko qasa wace tayi tanadi akan yan gudun hijira, game da yake yaken da ake fuskanta a duniya.

Anbar yan gudun hijira na wahala batare da tallafi ko taimako ba. Saboda haka dolene mugu tare mu tsira tare idan munki to zamuyi mummunar fadiwa.
Xan haka a wannan shekarar ina mika kokon barana a Majalisar dinkin Duniya saboda ganin rayuwar ‘yan gudun hijira ta inganta.

Muna so muga Karin wasu hanyoyi na taimakama ‘yan gudun Hijira dan ganin su ma rayuwar su ta in ganta kamar na sauran Mutane.
Saboda in dai za’a cigaba da yaki a Duniya to, dole a sami ‘yan gudun hijira.
Ina godiya da wannan rana ta tunawa da ‘yan gudun hijira ta Duniya.

Sakataren MDD ya nuna damuwa da karuwan rikici a Afirka

Daga Zubairu Muhammad

Mr. Antonio Guterres ya bayyana damuwarsa da yadda yawaitar karuwan asarar rayuka dake gudana a yankin Afirka.
Da yake magana a madadin Sakataren mai taimaka masa wajen yada labarai Mr.Oluseyi Soremekun
Yace; abin damuwane yadda ake samun karuwan rikici dake kawo zubar da jini masamman tsakanin Manoma da Fulani makiyaya a yammacin Afirika.

Babban Sakataren ya nuna matukar damuwarsa game da karuwar rikicin, musammamma yadda adadin ke karuwa a duk bangarorin Afurkan tsakanin Manomar da Makiyayan, kuma dangantakar kunlun kara lalacewa take yi, kuma gashi an ki yi ma Fulani Labi da wurin kiwo a wurare da yawa a Yammacin Afurka da kuma Afurka ta tsakiya. Ya yi Allah wadai da yawan asarar rayuka da ake samu, da barnata dukiya da kuma tabarbarewar zamantakewa, kuma hakan na kawo koma baya wajen karuwar Al’umma.

See also  Buhari allocates houses to 1994 Super Eagles squad

Tabarbarewar zaman lafiya ya shafi duk kusan ‘yan Afurka, hakan kuma ba karamin koma baya bane a yankin.
Sakataren ya nuna damuwarsa da yadda maharar suke kai hare hare masamman ga fararin hula alhalin dokar qasa da qasa ya haranta ire-iren wanda kuma yana ruguje manufofin kowani irin Gwamnati ko alumma, awdanda suke gudanar da ayyuka tare.
Dolene arikabin dokokin qasa da qasa wajen kare rayukan alumma na birni da qarqar.
Ya kara da cewa Majalisar dinkin duniya tana bukatar hadinkan alumma a kota ina dasu zama masu taimakon juna da agazamasu da ta hanyar samar da zaman Lafiya mai dorewa wanda zai kawo karshen zubar da jini .

Zamu zaburar da matasa su rika yin takarar kujerar Majalisa

Inji Mrs. Yetunde Bakare

Daga Zubairu Muhammad

Mrs. Yetunde Bakare itace Babbar mai gudanar da harkokin Kungiyar , cibiyar harkokin Wakilci ta Afirika wanda ake kira (YIAGA) a turance. Kungiyace mai fafutukar ganin cigaban matasa dake tasowa a nahiyar Afirika.
Da take jawabi wajen wani taron yayan kungiyar a zauren taro na Shehu Musa Yar’adua dake birnin tarayya Abuja cikin makon da yagabata.
Tace ; cikin shirye shiryen da kungiyar ke kokarin gabatarwa shine.
Cibiyar harkokin wakilci ta Afirika YIAGA ta kaddamar da wani tsari na taimakawa matasa xon yin takara a majalisu dokoki na Jihohi ko na tarayya, karkashin Kungiyar Tarayyar Turai EU. Wannan wani motsi ne na taimakawa matasa cin zabe a shekara ta 2019. Shidai wannan tsari na yanar gizo na dauke da cikakken sunayen matasa da zasu tsaya takara kuma zai zama hanyan Samar da ingantaccen kwarewa ga matasan yan siyasan.
Ta kara da cewa shirye muke mu tattauna da matasa dake sha’awar yin takarar a Nijeriya domin zavurar dasu da taimaka masu ta hanyoyin shiga siyasa da yadda zasuyi nasarar lashe zave a shekarar 2019

Wanan zaibaiwa matasa damar shiga a dama dasu a siyasan Nijeriya idan suka zama masu rinjaye a Majalisa.
Shirye muke damu nunatar dasu hanyoyin shiga harkan siyasa da basu taimako ana damawa dasu ,maimakon su zama yan rakiya ko bangar siyasa.
Munshirya basu goyon baya da nunatar dashi yadda ake yakin niman zave da kuma nuna amfaninsu a Majalisa.
Yanzu matasa suna da damar shiga Jam’iyyu da za’ayi dasu cikin harkokin siyasa. Saboda sune kashin bayan Damukurdiyya.
Manufar wanan taron shine bayyanar da yadda za’asamu cigaba a harkokin siyasa ta vangaren matasa.
Shirye muke mu yada wanan manufofin zuwa ko ina tahanyar motocin sufuri jiragen sama dama karkara. Kuma zamu kasance a tituna muyi tafiyar kilomitochi domin bayyanar da manufar wanan kungiyar. (YIAGA )

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here