Aikin Gwamnati yafi karfin ya’yan Talakawa a Mulkin Buhari

0

Aikin Gwamnati yafi karfin ya’yan Talakawa a Mulkin Buhari

Daga Zubairu Muhammad

labari da kafar yadda labarai ta Daily Trust ke cewa aiki a Gwamnatin Tarayya na nema ya zama kayan gabas inda sai su wane-da-wane su ke iya samu a wannan Gwamnati. ‘Yan Majalisu da manyan mylar a bran Gwamnati ne ke yin yadda su ka so.

Aikin Gwamnati ya zama na yaran manya a Najeriya
A halin yanzu sai dan Talaka yayi da gaske zai iya samun aiki ganin yadda Minstoci da Sarakuna da sauran manya ke hana a dauki yaran Talakawa. A cikin shekaru uku na Gwamnatin APC dai da wuya ka ga ana tallar bada aiki a Ma’aikatun kasa.

Manyan Ma’aikatu irin su CBN, NNPC, NDIC, FIRS, PTAD, da sauran su duk su na daukar aiki ne a boye. Hukumar FCC da ya kamata ace tana tabbatar da adalci ba ta aikin ta. Ana raba aikin ne dai ga ‘Yan Majalisu da ‘Yan fadar Shugaban kasa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya 183 cikin 185 da ake da su sun dauki mutane 13, 780 aiki a cikin shekaru 2. Daga ciki dai mutum 6, 917 da aka dauka ba su bi wata ka’idar daukar aiki na kasar ba kamar yadda ya dace.

A kwanaki dai Daily Trust ta rahoto cewa babban bankin Kasar watau CBN ya dauki mutum fiye da 900 aiki a boye. Haka dai wasu da-dama su ke yi ba tare da tallatar da cewa ana neman ma’aikata a gidajen Jaridu ba. Talaka dai na ganin ta kan sa a halin yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here