An umarci ya’yan PDP suyi zanga-zangan lumana a dukkan jihohi
Daga Zubairu Muhammad
Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa ya umurci ya’yan jam’iyyar na jihohi,tare da shugabanni da masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar da su fito su yi zanga-zangan lumana a hukumomin yan sanda dake dukkanin jihohin kasannan.
Acewarsa Jam’iyyar zata gudanar da zanga-zangar lumanane domin nuna rashin amincewa da irin cin zarafi da Rundunar Yan sanda ta gudanar kan ya’yan Jam’iyyar dama Gwamnan Jihar Ekiti a jiya Laraba.
Yace; wannan ba karamin cin zarafi bane da Yan sanda sukayi yayin da suka rika harbi kan mai uwa da wabi yayin da suka kewaye gidan Gwamnati a garin Ekiti batare da nuna wani daliliba.
Wanda a halinda ake ciki yanzu Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose yana nan Asibiti yana shan magani ta sana diyar wanan harin da aka kai gidansa.
A lokacin da yake bayani game da zanga zangar Sakataren shirye-shirye na jam’iyyar, Kanal Austin Akobundu (mai ritaya) a madadin Shugaban jam’iyyar ta bukaci dukannin ya’yanta na jihohi da su gabatar da wasikar zanga-zanga ga sufeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris ta hanyar kwamishinonin yan sandansu.domin nuna mashi halin da Jam’iyyar PDP ta shiga saboda abinda yan sanda suka aikata a fadar Gwamnan dake Jihar Ekiti