Rashin Biyan Haƙƙoƙin Ma’aikata: Ya Durƙusar da Gidan Rediyo Najeriya

0

Rashin Biyan Haƙƙoƙin Ma’aikata: Ya Durƙusar da Gidan Rediyo Najeriya.

Daga Bishir Suleiman

A ranar litinin ɗin nan ne, masu zanga zanga suka yi dafifi a farfajiyar tashar gidan Rediyo muryar Najeriya dake Kaduna (FRCN) Sakamakon kin kula da haƙƙokin jindaɗi da walwalar ma’aikatan tashar. Inda suka yi dafifi ɗauke da allunan ƙorafe ƙorafensu, suna kuma ta rera waƙokon begen gwamnati ta duba halin da suke ciki.

Wasu daga cikin allunan, na ɗauke da bayanan a kula da jin daɗin ma’aikata, a kuma dubi yanayin da suke gudanar da ayyukan nasu, tare da biyansu haƙuƙuwansu wanda suka shafe shekaru suna bi, tare da samar da kayayyakin aikin da za su ƙara bunƙasa tashar.

Wasu alluna kuwa na bayyana ɗumbin matsalolin da ma’aikatan ke fuskanta a lokacin aiki na rashin ababen zirga zirga.

Da ya ke magana a wajen gudanar da zanga zangar, shugaban ƙungiyoyin ƴanjaridu na ƙasa reshen jahar Kaduna, Malam Salisu Ibrahim, ya nuna cewa yin hakan zai janyo hankalin mahukunta kan duba halin matsi da rashin kula da ma’aikatan ke fuskanta, wanda ke tauye cigaban aiki.

Ya ci gaba da cewa jin daɗin ma’aikata, ba wani sabon abu ba ne a gwamnatance, da za a yi ta ce – ce – ku ce kansa a nan gida dama wajen ƙasar nan. Dan haka dan me gwamnatin tarayya ba za ta mayar da hankali kan wannan batu ba, muna fatan gwamnati ta dube shi da idan basira.

Kazalika, Daraktan da ke kula da shiyar Kaduna, na Rediyon tarayyar Najeriya, Malam Buhari Auwalu, ya bayyana jin daɗinsa kan yadda aka gudanar da zanga zangar a cikin lumana, ya kuma ƙara da cewa ” Tabbas! Kafafen yaɗa labarai suna buƙatar a ɗaɓɓaka su da kayayyakin aiki na zamani.

Inda sauran gamayyar ƙungiyoyi da suka maganta, sun nuna akwai ƙalubale da dama ga gwamnati a wannan ɓangare, dan haka, sai gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen bunƙasa hanyoyin sadarwa na ƙasar nan. Dan kuwa, Hausawa kan ce ” Tun kafin a yi da kai, ka yi da kanka” ƙungiyoyi da dama na taka muhimmiyar rawa a wannan fanni, wanda majalissar ƙasa na da gaggarumar rawar da za ta iya takawa a kan lamarin.

Shugaban shiyyar ya buƙaci ma’aikatan da su ƙara haƙuri, za su ga canji nan ba da jimawa ba, kuma ya alƙawarta miƙa takardar kuken tasu ga inda ta dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here