DOLE NE MU CIYO BASHI DON AYYUKAN RAYA KASA DA MANYAN AYYUKA

0

DOLE NE MU CIYO BASHI DON AYYUKAN RAYA KASA DA MANYAN AYYUKA

inji – Buhari
Daga Zubairu Muhammad

– Shugaba Buhari ya bayyana wa AFREXIM zaici gaba da neman taimakon su wajen gyara ga lalatattun kayayyakin kasar
Karku gajiya damu saboda zamuyi ta zuwa, muna rokon ku daku yi mana sauki

Mun Fahimci cewa muna bukatar kudin da zamu gyara titina, hanyoyin jirgin kasa, wuta da kuma hanyoyin sadarwa

A ranar Alhamis ne Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana wa wasu mambobi AFREXIM cewa zaici gaba da neman taimakon su har zuwa sanda zai kawo karshen gyararrakin da zai gudanar a kasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin da bankin yakai masa ziyara a Abuja karkashin jagorancin Mr. Benedict Okey.

Jawabin na Buhari ta bakin Shehu Garba mataimaki na musamman a bangaren kafofin watsa labarai yace” muna godiya da irin taimakon da kuke bamu sannan zamuci gaba da zuwar muku har zuwa kawo karshen matsalolin mu”.

See also  DINGYADI HANDS OVER 10,635 BULLETPROOF VESTS TO NPF

“Mun Fahimci cewa muna bukatar kudin da zamu gyara titina, mu samar da hanyoyin jirgin kasa, wuta da kuma kafofin sadarwa, saboda haka karku gajiya damu saboda zamuci gaba da zuwar muku, muna rokon ku daku saukaka mana”.

Shugaba Muhammad Buhari yace kasar tana fuskantar matsaloli na gyare gyare da wanda zamu nemi abokan ciniyya masu gwabi.

Shugaba kuma ciyaman na AFREXIM Dr Oramah ya bayyana jindadin su sannan da kuma goyan bayansu ga gwamnatin Nageriya wajen aiki da bankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here