Gasar cin kofin duniya kasar Croatia tayi bazata zuwa wasan karshe
Daga Zubairu Muhammad
Kungiyar kwallon kafa ta kasar Croatia tayi bazata daba ayi tsammaniba inda ta kece tsara sama da kasa ta ketare zuwa wasan karshe na cin kofin duniya dake gudana a kasar Russia.
Kasar Croatia wanda take rukuni daya da kasar Argentina da Nigeria Iceland tayi abin azo agani Wanda tabaiwa alumman duniya mamaki. Kasar ta Croatia babu wanda ya kawota cikin jerin kasashen da zasu buga wasan karshe, saboda ana mata ganin rabonta da zuwa matsayi makamancin wanan, tun shekara 1950.
Croatia tana daya daga cikin yammacin Turai da sukayi bajinta wanda dole a yabamata.saboda ta kara da kasashen da ake ganin manyane amma ta lallasasu .
Yanzu dai tana shirin fafata wasan karshe tsakaninta da kasar France,
Kafin ta qaraso wanan matakin kasar Croatia ta doke Nigeria da Argentina da Denmark da Uruguay sannan ta doke kasar England