Kungiyoyin MDD dana Afirika sun gudanar da taron karawa juna sani karo na biyu

0
  1. Kungiyoyin MDD dana Afirika sun gudanar da taron karawa juna sani karo na biyu

Daga Zubairu Muhammad

Cikin makon da tagabatane kungiyoyin guda biyu na Majalisar Dinkin Duniya (UN)da takwararta Kungiyar Hadaka (AU)ta Afirika suka gudanar da babban taro wanda aka kirashi da taron karawa juna sani karo na biyu .

Taron wanda aka yi shi a ranar 9 ga watan Yuli, 2018, a karkashin jagorancin babban mai tsare-tsare ta kungiyar Afirka Moussa Faki Mahamat, da babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.

Taron dai ya gudana ne a babbar Hedikwatar kungiyar Afurkan da ke Birnin Addis Ababa ta kasar Ethiopia wanda ya sami halarcin Mutane daga kasashe daban-daban na Duniya.

Wadada suka zama manyan baki a wurin taron su ne shugaban tsare-tsaren kungiyar Afurka, Moussan Faki Mahamat da Babban Sakatare Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres duk sun gabatar da jawabin maraba da baki, sannan kuma sun nuna matukar farin cikin su game da wannan taron, sun ce za su yi aiki tare tsakanin wadan nan kungiyoyi guda biyu,wajen bunkasa aiyukan Gwamnatocin Duniya baki Daya.

Shi dai wannan taron karawa juna sani kashi na Biyu ya mai da hankali ne akan yadda kungiyoyi biyun za su hada hannu su yi aiki tare wajen samar da zaman lafiya da kuma harkan tsaro a fadin Duniya,

sun kuma tattauna irin cigaban da aka samu a taron da ya gabata, sannan kuma sun gabatar da wasu kudiri na cigaba wanda ake so ya zama sun kankama a shekarar 2030.da kuma 2063

Kungiyar AU da ta UN din kuma sun yi Magana akan yadda za su inganta alakar su wanje samar da hadin kai da gudanarwa wajen nemo hanyoyi dauwamanmu na warware matsaloli a kan ka’idan da suka shimfida a tsakanin su.

ka’idojindai sun hada kamar wasu damarmaki da ake samu, da kuma rabon kan iyakan kasashen Duniya, da kuma daukar mataki na gaggawa wanda ka’iya tasowa a tsakanin kasashe na tashin hankali, da kuma kare kara faruwan hakan a gaba, a kuma sa’ido sosai wajen zaman lafiya tsakanin kasashen Duniya.
Taron kuma
Taron ya nuna matukar damuwa akan yadda kasashe basa son bin doka da oda, sannan an nuna matukar damuwa akan barkewar rigingimu da kuma rashi tsaro a fadin Duniya gaba daya.

See also  INEC TA DAGE DUKKAN ZABUBBUKA CIKE GURBI SABODA TARZOMAR END SARS

Xan haka suka ce ya zama wajibi a kara inganta al’adu, ka’idoji, da kuma dokoki a Duniya gaba daya.

A nasa jawabin Sakataren majalisar dinkin Duniyar yayi akan a kara samar da wasu hanyoyi na dabaru wanda za su rinka dakile tashin hankali a cikin Duniya, ya kuma bada shawaran da a kara inganta siyasar Duniya, sannan mutane su rinka girmama doka, dan da haka ne kawai za’a samu dauwamanman cigaba a Duniya.

Ya kara da cewa; ya duba wasu hanyoyi wadanda suke kawo tsaiko ga zaman lafiya da harkokin tsaro a yankin Afurkan, an dai duba abubuwan da ke faruwa a kasashe kamar irin Burundi, Afurka ta tsakiya, yankin Kogin Chadi, Kamaru, Congo, Madagascar, Mali da kuma Sudan ta Kudu. An yi ittifaki akan cewa za’a kara ba da goyon baya waje shawo kan matsalolin da yankunan ke fuskanta, musamman abun da ya shafi tattalin arziki, da kuma kawo abubuwan cigaba a wadannan kasashen, sannan kuma ya kamata a girmama harkar siyasa a yankunan. Sai kuma batun yankin Sahel da aka tabo wanda sakataren ya ce majalisar Dinkin Duniya suna goyon bayan matakan da ake dauka, dan haka za’a kara hada hannu wajen kara inganta matakan.

Haka zalika Sakataren Majalisar dinkin Duniyar ya yabama jami’an tsaron kasashen Duniya ne wajen yadda suke sadaukar da kansu wajen kare al’umma, gaskiya sun cancanci a yaba musu.

Shima cikin jawabinsa, Shugaban tsare_tsaren kungiyar Afurkan ya yaba da matakin da majalisar dinkin Duniya suke dauka a game da rikicin Libiya, ya ce matakin ya nuna yadda majalisar dinkin Duniya take aiki tukuru akan al’amuran da suka shafi Duniya.

Sannan ya yaba ma kungiyar AU din yadda suke aiki ba dare ba rana wajen dakile fitintinu da suke faruwa a Afurkan, duk da matsalolin kudi da suke fama da shi, ya ce a shekarar 2016 sun warware matsaloli ki manin 2320, a 2017 kuma sun warware matsaloli 2378, dan haka wannan abun a yaba musu ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here