YA YA MAKOMAR MAKARANTAR MALLAM ADAMU CIROMA ZA TA KASANCE?

0

YA YA MAKOMAR MAKARANTAR MALLAM ADAMU CIROMA ZA TA KASANCE?

Daga Ibraheem El-Tafseer

Makarantar Marigayi Mallam Adamu Ciroma dake garin Potiskum, mai suna ‘Ciroma Ibrahim Islamic Primary and Secondary School’ tana daya daga cikin makarantu da suke bada karatu mai inganci ga dalibai a cikin makarantun da suke garin Potiskum. Duk da ba kyauta ake karatu a makarantar ba, amma ba kudin kirki ake karba a hanun iyayen dalibai ba. Mallam Adamu Ciroma shi ne ya dauki nauyin makarantar gabadaya, tun daga gine-ginenta har zuwa biyan kudin Malaman makarantar. Mafi yawan daliban makarantar ‘ya’yan talakawa ne, masu qaramin qarfi, ganin ga shi yanzu ya rasu, ko ya ya makomar makarantar za ta kasance?

Wakilinmu ya yi tattaki har zuwa makarantar, inda ya tattauna da shugabar makarantar Hajiya Fatsima Alhaji Mamu, inda suka tattauna, ta shaida masa cewa “Wannan makaranta an bude ta ne a shekarar 2004, wato shekaru 14 kenan. Mun fara da dalibai kadanne a wancan lokacin. Sannu a hankali makaranta tana girma har ta kawo zuwa yanzu. Muna da bangare uku ne a wannan makaranta, akwai bangaren yara Firamare, akwai kuma Sakandire. Sannan akwai karatun manya da ake yi wato ‘Adult education’ akwai kuma bangaren matan aure da suke zuwa karatun Alqur’ani a ranakun Asabar da Lahadi. Sannan akwai yara ‘yan Tahfizul Qur’an. A yanzu haka muna da Malamai 111 da kuma dalibai kusan dubu hudu (4,000)”.

Malama Fatsima ta qara da cewa “muna da ajujuwa 21 da multipurpose laboratories, wanda ya qunshi Biology, Physics da Chemistry. Sannan muna da computer center guda 2 da kuma dakin jarabawa (exam hall) guda 2 da dakin karatu (library) da kuma Staff room 2. Mallam Adamu Ciroma ya gina makarantar nan ne Fisabilillahi, domin ya taimaki ‘ya’yan talakawa. Kudin da ake karba a hanun dalibai bai ta ka kara ya karya ba. Kuma a hakan wasu iyayen yaran basa iya biya. Sai ka ga yaro ya gama Firamare amma sau daya ya taba biyan kudin makaranta. Kuma daliban da suka fara rubuta jarabawar kammala sakandire a wannan makaranta, Marigayi Madakin Fika, Mallam Adamu Ciroma shi ne ya biya musu kudin rubuta WAEC da NECO dukkansu”

Wakilinmu ya tambayeta, ganin cewa kudin da ake karba a hanun dalibai qalilan ne, ko ta ya ya ake biyan Malaman wannan makaranta albashi? Sai Hajiya Fatsima ta ce “wallahi, wallahi, wallahi kuxin da ake biyan Malaman wannan makaranta ba daga kudin da ake karba a hanun dalibai bane, Marigayi Mallam Adamu Ciroma shi ne ya ke biyan kudin albashin wadannan Malamai tun daga lokacin da aka bude ta har zuwa yau. Wata yana da kwana 16 Mallam ya ke turo Miliyan daya da dubu dari uku (1.3 Million), kudin biyan Malaman wannan makaranta. Wallahi bai taba fashi ba har zuwa rasuwarsa. Abin da yasa ya ke biyan albashi tun wata yana 16, ya ce haka ne tsarin biyan albashi a farkon tsarin aiki na qasar nan. Kudin da muke karba a hanun dalibai da su ne muke ‘yan gyare a wannan makaranta, kamar irinsu Fankoki, litattafan karatun yara da sauran abubuwa”

Wakilinmu ya qara tambayarta cewa, da yake marigayi Madakin Fika shi ne ya ke daukar aawainiyar wannan makaranta, abin da ya shafi gine-gine da biyan albashin Malamai, kuma ga shi yanzu Allah ya masa rasuwa, ko ya ya makarantar za ta kasance a yanzu? Sai Hajiya Fatsima Mamu ta ce “wannan shinan gaibu sai Allah! Tun da Mallam ba ya nan, muna roqon Allah yasa a cikin mutanenmu a samu wanda zai dauki wannan dawainiya. Mun kai kukanmu a wajen mai martaba Sarkin Fika, mun shaida masa matsalarmu. Mun je mun kai masa damuwarmu, ‘ya’yan talakawa sun fara kuka, kuka da hawaye sosai, suna fadin cewa shikenan makaranta ta tsaya, za a koresu a rufe makarantar. Na ce insha Allahu baza a rufe makaranta ba, kuma baza a kori dan kowa ba, kuma duk shirin da za ayi bazai fi qarfin dan talaka ba. Ni ko a biya ni ko kar a biya ni, zan tsaya na bautawa wannan makaranta har tsawon rayuwata, da izinin Allah. Abin da muke buqata ga iyayen daliban wannan makaranta, shi ne su bamu hadin kai. Dukkanmu Malaman wannan makaranta muna shirye da mu cigaba da koyarwa a wannan makaranta, insha Allahu makaranta baza ta tsaya ba. Ba ni kadai nake da iko a wannan makaranta ba akwai shugabanni, idan an zauna bamu san wace shawara za a tsayar ba”

“Ba mu sani ba ko akwai wasiyya da shi Mallam Adamu ciroma ya rubuta ya ajiye game da ci gaba da gudanar da wannan makaranta, amma matarsa Hajiya Inna Ciroma ta ce tana sane da wannan makaranta kuma za ta zo ta duba, ta ga wane irin gyare-gyare za a yi don cigaba da gudanar da ita wannan makaranta” inji shugabar makarantar Hajiya Fatsima Alhaji Mamu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here