Daktan Tsalakawa yayiwa mutum 4000 aikin kiwon Lafiya kyauta a Nasarawa

0

Daktan Tsalakawa yayiwa mutum 4000 aikin kiwon Lafiya kyauta a Nasarawa

Daga Zubairu Muhammad

Kwararen Likitannan da akewa lakabi da Dakotan Talakawa mai suna Hon. Joseph Haruna Kigbu yayiwa duban alumma aikin kiwon Lafiya kayuta .

Ayyukan da Likitan yayi ga alumma Wanda ya gudana kwanaki a karamin Asibitin dake Fadar mai martaba Sarkin Lafia Dr. Isa Mustapha Agwai dake garin Lafian Barebari.
Kwararen Likitan wanda yake jagorantar Likitochi na cibiyar kiwon Lafiya kyauta ta Afirika da ake kira (Doctor on the move Africa) ya kwashe shekaru da dama yana gudanar da wanan harkan kiwon Lafiya kyauta.
masamman ga tsalakawa a Jihar Nasarawa.

Wanannema yasanya alumma kemasa kirari da wanan sunan cewa Dakton tsalakawa.

Da yake jawabi a gurin taron tsohon Dan majalisa mai wakiltar mazaber Lafia da Obi Hon.Joseph Haruna Kigbu yace; wanan shirin ya dade da gudanarwa kamar yadda kowa ya sani a nan kuma munayinsane domin taimakawa talakawa marasa galihu kai harma da masu arziki.kuma duk cutar dayake damin mutum idan ya zonan da yardan Allah zamuyi masa magani.

Akwai bangarori dabam dabam na likitochi da muke tare
Akwai masu aikin IDO yanar IDO idan aiki za’ayi zamuma mutum aiki. Idan kuma magani zamuba mutum to awakishi idanma tabarau na hangen nesane duk mun tanedeshi.

Idan kuma bamgaren Tiyatane akwai likitochi maza da mata saboda haka muna bukatar alumma su bamu hadinkai wajen gudanar da aikinmu zamuyi kwana uku akwai kati idan mutum ya karbi kati yaje a auna jininsa sannan yaje wajen likita ya duba maike damunsa idan yakama sai anyi aikine ma’ana tiyata sai yaje bangaren tiyata idan magazine sai aje bamgaren ansan magani.
Yara kanan wanda suke da karancin shekaru basai anyi awan jiniba saboda yara basu da hawan jini.sai dai idaan tiyatane a kaisu wajen gwajin jini .
Shima da yake jawabi a gurin taron Sarkin Lafia Dr Isa Mustapha Agwai wanda Madakin Lafia Alhaji Isyaka Dauda yayi jawabi a madadinsa ya nuna jindadinsa da irin tallafin da Dakotan Talakawa ke baiwa alumma .

Yace; babu abinda yakai Lafiya dadi duk arzikinka idan baka da Lafiya bazakaji dadin arzikinba.
Saboda haka muna rokon jama’a subada hadin kai wanan tallafin da aka kawo an kawone saboda su amma idan basubada hadin kaiba bazasu mureshiba .
Anyi nasarar yiwa mutani sama da dubu hudune suka amfana da wanan tallafi na kiwon Lafiya da ya gudana .inda akayi tiyata ga cututuka dabam dabam kama daga IDO,kunni,Qaba, HIV,TV,da masu cutar kashin kafa dake hana tafiya,da sauran cututuka. Maza da mata manya da yara kanana suka samu tallafin.

See also  Pantami Receives American Multinational Financial Services Corporation (Visa Inc)

Taskar labarai tasamu zantawa da wasu da suka amfana da wanan tallafin
Hajiya Hasana tace ; mahaifiyatace take fama da lalura na idanunta duka biyu kuma munje Asibiti anyi tayi abin ya gagara an turamu Asibitin IDO a Kaduna amma bamu da kudi, yanzu gashi anyi mata aiki kyauta kuma ambata magunguna da zata rika amfani dashi. Sannan yarona yana fama da cuta a mazakuntarsa shima anyi masa aiki kyauta. Hasana ta fashe da kuka tayi adu’ar Allah ya sakawa Dr.Haruna Joseph Kigbu da alheri .saboda ya ceto rayuwar mahaifiyanta da danta.
Shima Alhaji Umar Abdullahi wanda akayimasa aiki a bayansa yace ; Asibiti sunce sai ya biya #150,000 amma bashi da kudin gashi anyi masa aiki kyauta yana godiya ya kara dacewa munji ance Dakton Tsalakawa ya sake fitowa takarar Dan majalisa to zamu zabeshi saboda mai tausayinmune.
Itama Debura Agye tace ; nayi fama da cuta a cikina nayi yawo a Asibiti na hakura bamu da kudi ,yau gashi nayi bankwana da wanan cutar Allah ya sakawa Dr Haruna Kigbu da alheri .
Sama da mutum daribiyune akayimasu aikin IDO kuma sunyi godiya da sa albarka.
Dr.Haruna Joseph Kigbu a baya ya taba wakiltar alumman mazaber Lafia da Obi a majalisar wakilai na tarayya daga shrkarar 2011zuwa 2015 inda ya kara lashe zabe amma akayi masa magudi yace yabarwa Allan.
Yanzu haka ya sake tsayawa takara domin maimaita wanan kujerar.duk da dai yace zuwansa Majalisa ba domin samun kudi bane zamansa a gurin wani gulbine na taimakawa alummma da aikinyi da kuma samar masu abubuwan sana’a domin baya bukatar ganin alumma suna gudanar da rayuwa cikin kunci.
Yanzu haka Dokton talakawan yanana yana gina katafaren Asibiti da akawasuna Asibitin talakawa a garin Lafia

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here