WANI YA HADDASA RIKICIN DA AKA TSARE DAN MAJALISAR DUTSI.

0

WANI YA HADDASA RIKICIN DA AKA TSARE DAN MAJALISAR DUTSI.

Magoya bayan Dan majalisar karamar hukumar Dutsi ta jahar Katsina…Wanda kotu ta tsare a gidan yari na kwana Daya..sun zargi wani jigo a gwamnatin APC ta Katsina shine ummul haba isin rikicin siyasar ta Dutsi..Wanda har ya Kai ga zuwa wajen Yan sanda da kuma kaishi kotu.wanda aka kaishi gidan yari shida abokan siyasar shi.kuma Jami ai a reshen jam iyyar na Dutsi
Suka ce abin da ya faru shine.lokacin zaben shugabannin jam iyya.na karamar hukumar Dutsi.aka baiwa” wani Mai suna Rabo ado.kayan zabe.wanda bashi ya Kamata a baiwa” ba..
Wannan ta haifar da rikici…Wanda ya Kai ga.shi Dan majalisar ya dauko rabo Ado a motarsa ya kawo shi gidansa dake rukunin gidajen Yan majalisa na Katsina.
Sai abokan adawarsa suka ce ya sace Rabo ado.suka Kai Kara a gaban Yan sanda.wannan shine mafarin rikicin.inji su
Abu kamar ya wuce.sai aka ci gaba da maganar Wanda har ta Kai ga tsare Dan majalisar a gidan yari a ranar Alhamis..13/ Yuli/ 2018. Domin kawai a muzanta shi.
Sun ce an bada belinsu ..Bayan an saka baki daga bangarori da yawa Amma za a koma Don cigaba da shara ar nan gaba kadan
Ana tuhumarsu da cin mutuncin Rabo ado.da tsare shi ba Bisa kaida ba..
Magoya Bayan sun ce duk wannan kutungwaila ce ta wani kusa a jam iyyar da gwamnatin ta jaha.kuma sun barshi da Allah.. siyasar Dutsi kuma Zasu rike wuta .Babu Mai Yi masu cushe ko dankaro wani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here