AMBALIYAR RUWA DA ISKA YA JAWO ASARAR RAYUKA DA GIDAJE A KARAMAR HUKUMAR JIBIYA JIHAR KATSINA.

0

AMBALIYAR RUWA DA ISKA YA JAWO ASARAR RAYUKA DA GIDAJE A KARAMAR HUKUMAR JIBIYA JIHAR KATSINA.

Daga​ Idris Muhammad Bella

Al’ummar Yankin Kukan Dan Maciji da ke Karamar Hukumar Jibiya Jihar Katsina sun wayi gari cikin Mummunan tashin hankali sakamakon Iftila’in Ruwan sama da iska mai Karfi da aka yi a daren Jiya Lahadi wanda ya janyo musu hasarar Rayuka masu yawa da kuma Dumbin Dukiya masu tarin yawa.

Ya Zuwa yanzun dai da ake tattara wannan rahoton ba’a iya kididdige adadin Rayuka da kuma Gidajen da suka Salwanta ba a sakamakon wannan Iftila’i da ya afka wa Al’ummar wannan yanki wadanda dayawa masu kananan karfi ne, ba su da ko dan abinda za su saka a bakinsu sakamakon rashin karfi da kuma yanayin Halin Rayuwa da ake ciki.

Da wannan mu ke mika Kokon Bararmu ga ita Gwamnatin Tarayya da ma ta Jihar Katsina da duk wasu masu hannu da shuni, da su taimaka du Tallafi Rayuwar wadannan Bayin Allah domin suna bukatar Taimako matuka gaya.

Muna Rokon Allah ya kiyaye afkuwar haka gaba, Allah ya yafe mana laifukanmu yasa mu ga karshen Daminar nan Lafiya Amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here