Buhari ya jefa alumman Nijeriya cikin wahala

0
720

Buhari ya jefa alumman Nijeriya cikin wahala

Inji Kabiru Turaki
Daga Zubairu Muhammad

Dan takarar Shugabancin kasa qarqashin tutar Jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Kabiru Tanimu Turaki yace; a halinda ake ciki yanzu alumman Nijeriya suna da nasanin zaben Shugaban kasa Muhammad Buhari sakamakon yadda sukayi tsamanin idan sun zabe shi komai zai sauya abin ya gagara.

Yace; alamun da Buhari yanunawa alumman kasannan yayi masu karya.saboda a lokacin yakin niman zabensa yace; idan alumman Nijeriya suka zabeshi a matsayin Shugaban kasa zai kawo sauyi da saukin rayuwa saboda zai rage farashin man petur zata koma qasa da #87 sannan farashin Dala zai koma daidai da naira ($/#)sanan zai gyara tattalin arziki abinchi zaiyi sauki zai magance matsalar tsaro masamman na kungiyar Boko haram.

Amma yanzu halin da ake ciki alumman Nijeriya sun gwammace gara rayuwarsu na baya kafin hawa mulkin Buhari.
Dan takarar yace; yanzu Dalan Amurka ta ninka darajan naira sau uku sannan man petur yanzu ya haura fiye da baya an ninka kudinshi.
Tattalin arziki ya lalace abinci yayi tsada talaka na fama da wahala da yaunwa .
Ya kara da cewa yanzu alumman qasannan suna fama da matsananciyar yaunwa ga bala’i ta kungiyar Boko haram. Yace; ada rikicin Boko haram ana san yana faruwa ne a gabashin Nijeriya , amma yanzu yana kokarin mamaye arewaci gabaki daya.
Barista Kabiru Turaki ya kawo misali da guraren da a baya basusan wani rikiciba amma yanzu rigima yana mamayansu kamar Jihar Zamfara da Sokoto inda ake kai hare- hare ana kisan alumma kuma babu abinda Gwamnati tayi akai.
Yace; Gwamnatin APC ta kwashe jami’an tsaro sama da 30,000 takaisu Jihar Ekiti saboda tayi magudin zave amma ta kasa kai jami’an tsaro Jihohin Zamfara Sokoto Kaduna Nasarawa Benuwe Taraba Adamawa Plateau guraren da yanzu haka ake kisan alumma.
Yakara da cewa ; manyan mutani a qasannan da sarakuna sun tabbatarwa alummansu cewa Gwamnati bazata iya karesuba saboda haka su mike tsaye sukare kawunansu.
Yace; alumman Nijeriya sunyi zaben tumin dare yanzu da nasanin zaven shi, saboda ya turasu cikin wahala da talauci da rashin aikinyi.
Sannan yayi kira ga alumman Nijeriya dasu fito kwai da kwarkwata a zaven 2019 su zave jami’iyyar PDP saboda itace ta dace da mulkin Nijeriya.
Barista Kabiru Tanimu Turaki ya bayyana hakane a zauren taro na Jami’iyyar PDP dake garin Lafia Jihar Nasarawa a lokacin da yaje gudanar da yakin niman zabensa a matsayin Dan takarar Shugaban kasa a zave mai zuwa.
Yace; jam’iyyarsa zata gyara kurakuranta zata kuma samar da aikinyi kamar yadda tasaba ga alumman Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here