An Yiwa Dan Shekara Uku Kisan Gilla A Garin Potiskum.

0

An Yiwa Dan Shekara Uku Kisan Gilla A Garin Potiskum.

Daga Sani Hamisu.

Wani abin ban Tausayi da kuma abin al ‘ajabi da ya faru a garin Potiskum ta jahar Yobe. Inda aka samu wani mutumi ya caccakawa wani yaro dan shekara uku wuka a kirjin sa.

Shidai wannan yaro mai Suna Abubakar Abdussalam Bello ya samu ajalinsa ne a hannun mijin mamansa da ya Auri mamansa bayan sun rabu da mahaifinsa, wato shekara biyu da suka wuce.

Al ‘amarin de ya faru ne yau Talata, shi mutumin yana Auren Mamar yaron, maman yaron sun samu matsala da mijinta dan haka ya farma yaron da wuk’a wajen sukan yaron a k’irji har sanda yaga ya daina motsi, sannan ya fito da niyar gudu, inda makwacciyarsu ta biyo bayansa da gudu tana ihun aka wo taimako har jama’a suka cim masa, .

ita kuwa maman yaron a take ta faďi k’asa sumammiya bayan idonta sunyi arba da gawan danta cikin jini,

Yanzu haka an mik’a wannan mutumi a hannun y’an sanda dake garin potiskum yayin da shi kuma yaron aka garzaya dashi Gidan Alh Bello dake garin Potiskum dan yi masa sallah kaman yadda addini ya tanadar,

Ita kuma mahaifiyar yaro an garzaya da ita babban asibitin dake garin Potiskum dan ceto rayuwarta

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here