Majalisar Dinkin Duniya ta mikawa Jihar Adamawa kayayakin ginin babban Kotu

0

Majalisar Dinkin Duniya ta mikawa Jihar Adamawa kayayakin ginin babban Kotu

Daga Zubairu Muhammad

A ranar Asabar da ta gabata ne Jihar Adamawa ta samu sababbin kayayyakin aikin gina babban Kotu daga Masalisar Dinkin Duniya. Bangaren da ke kula da ‘yan gudun hijira na Masalisar Dinkin Duniyar ne suka mikama Jihar Adamawan kyautar kayayyakin ta hannun babban mai kula da yankin Brigaitte Mukanga-Eno.

Mukanga-Enon ta ce “mun ba da wannan kayan ne domin inganta aikin wannan Kotun ta Majistire a wannan Karamar Hukuma ta Ganye xan ta koma Babban Kotu (High Court), saboda yadda Masalisar dinkin Duniya ta ke goyon bayan bangaren shari’a musammamma ganin jihar Adamawa na daya daga cikin yankin da ke fama da matsalar tsaro a Najeriya.

kuma hakan zai ba da daman kare hakin dinbin Mutanen da ke yankin, musammamma ‘yan gudun hijira da ake yawan zalintar su. Yanzu haka muna da ‘yan gudundun hijira wadanda suka yi rijista a wannan jihar kimanin 73,000,

kuma 20,000 daga cikin su sun dawo gida, dan haka wannan Kotun za ta taimaka musu idan suna da wani koke na danne musu haki, saboda dama daga cikin su yanzu an kwace musu filayen su da ka yayyakin su, wanda kuma ya kamata a dawo musu da a bunsu”.

A lokacin da ya ke Magana a karamar hukumar Ganyen Matemakin Gwamnar Jihar Adamwan Injiniya Martins Babale, ya yi matukar nuna farin cikin shi game da yadda aka sami babban Kotu ta farko a karamar hukumar Ganyen.

Ya ce muna fatan jama’ar karamar hukumar Ganye za su ba da hadin kai wajen samun nasarar kamala wannan babban aikin. Ya kara da cewa “Jihar Adamawa a shirye ta ke wajen goyon bayan bangaren shari’a”.

Su ma a nasu bangaren Babban Antonin shari’a da Kwamishinar Shari’ar jihar Adamawan Bala Silas Danufi sun nuna matukar farin cikin su da samun wannan babban koto ta farko a karamar hukumar Ganye ta Jihar Adamawan.
A inda suka ce Kotun za’ayi amfani da ita wajen kwato ma mata hakin su na abun da ya shafi fade da kuma nuna musu babbanci da ake yi.
Su ma Sarakunanar Gargajiya da Shugaban qaramar hukumar Ganyen sun jinjina wa Majilisar dinkin Duniya da suka tabbatar masu da mafarkin da suka dade suna yi na samun babban Kotu a qaramar Hukumar Ganye ta farko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here