An Damƙe Shaharun Mayaudaran dake Yaudarar Direbobi suna ce masu Motoci.
Rundunar Ƴansandan jahar Katsina, ta bayyana wa manema labarai a wata takarda mai lamba CZ:5250/KTS/PPRO/VOL/2/27 da Kakakin rundunar ya sanya wa hannu.
Rundunar ta bayyana a ranar 7 ga watan da muke ciki, a samu nasara damƙe wasu shahararen mayaudara da suka gwanance wajen yadarar masu Motoci ta hanyar zuba masu abin da ka sa bugarwa a cikin abin sha, dan sace wa jama’ah, motoci.
A wani aikin haɗin guiwa da ƴansanda suka aiwatar a ranar 6/7/2018 a wajejen ƙarfe goma, ƙasurgumin mayaudarin ya nemi Halili Aliyu direban tifa kirar Man Dizal da kuɗinta zai kai Naira Miliyan Takwas da yaron motar Kabir Musa dukkan su ƴan ƙaramar hukumar Dutsinma, da su ɗebo masa tifar ƙasa, inda bayan an gama ɗebo masa ƙasar sai ya mayaudari ya kawo abin sha mai ɗauke da gubar da ka sa bugarwa a cikin abin sha, ya baiwa da direban sannan ya gudu da motar.
Waɗanda ake zargi da aikata laifin su ne Murtala Yahaya wanda ya ke a ƙauyen Maigandi da ke ƙaramar hukumar Funtua ta jahar Katsina da kuma Adekunle Adegbola da ke titin Kaduna jakshin suleja ta jahar Niger, yansandan da ke sunturi a kan hanyar ne suka damƙe su, a lambata ta jahar Niger tare da tifar.
Ana ci gaba da tsananta bincike dan damƙe sauran waɗanda ke da hannu a cikin aika aikar.
Cewar kakakim Rundunaf SP Gambo Isah: A mamadin Kwamishinan Ƴansandan jahar Katsina.