BUDADDIYAR WASIKA GA GWAMNA DA KUMA GWAMNATIN JIHAR KATSINA

0

BUDADDIYAR WASIKA GA GWAMNA DA KUMA GWAMNATIN JIHAR KATSINA

Assalamu Alaikum warahmatullah, bayan gaisuwa irinta addinin islama, cikin ladabi da girmamawa ga gwamna *Aminu Bello Masari* Da kuma gwamnatin jihar Katsina na zabi wannan kafa ta yanar gizo domin itace hanya mafi sauqi a gareni da zan isar da saqon al’ummar garin “YANKARA”

Maigirma gwamna, garin “YANKARA” garine mai tsohon tarihi da kuma tarin albarkatun noma, wandan kusan a qalla kashi casa’in bisa dari na al’ummar garin duk manoma ne masu dan qaramin karfi, a wannan fanni na noma suke bayar da gudunmuwa gaya wajen ganin sun farfado da darajar noma da tattalin arzikinmu na najeriya, kamar yanda shugaban qasa *Muhammadu Buhari* Ya buqaci al’ummar najeriya.

Maigirma gwam na, al’ummar garin YANKARA sun kasance masu matuqar tarin yawa da suka fito kwansu da kwarkwata domin bada gudunmuwa domin ganin an kafa wannan gwamnati da suke da yaqini za’ayi musu adalci a dukkan al’amuransu na yau da kullum,
Maigirma gwamna ba tare da bata lokaci ba, Dalilin dayasa na rubuta maka da gwamnatin jihar Katsina wannan wasiqa tawa shine:

Muna roqonka dan girman Allah kasa a biya mutanenmu diyyar gonakinsu da aka lalata a sakamakon aikin hanyar da gwamnatin jihar Katsina ta bayar daga garin Yarmalamai zuwa Yankara, Mai girma gwamna abinda ya qara tadawa al’ummar wannan yanki namu hankali musamman masu wadannan gonaki shine, ba’a sanar dasu cewa za’a fara wannan aikin ba, bayan duk saida shukarsu tayi girma sosai watama harta fara qosawa, kuma har ila yau babu wani tabbaci dake nuni cewa za’a biya mutanen nan haqqoqansu domin ba’a auna ko daukar sunayen masu gonakin a hukumance ba.

See also  FG, IFAD train 98,000 rural farmers

Maigirma gwamna, a binciken da muka gudanar munsamu labarin cewa mafi akasarin wadanda abin ya shafa da Allah suka dogara dakuma wannan dan noma suka dogara, domin ta nan ne suke ci su sha suyi sauran hidindimun yau da kullum, duk a cikin wannan bincike namu mun gano cewa mafi akasarin wadannan manoma sun ciyo bashin irin shuka, takin zamani, feshi da sauransu daga qungiyoyi irinsu Lafoo, wacot, bank of agriculture (B.O.A) da sauransu. Maigirma gwamna ba fata muke ba amma idan har ba’a biya wadannan mutane haqoqansu ba to wallahi zasu kasance cikin mawuyacin halinda sai dai muce Allah ya kyauta.

Da wannan muke kira ga gwamna ka dubi girman Allah kasa a biya wadannan mutane haqqoqansu domin sawwake masu wannan hali na qunci da suka samu kansu, Ka huta lafia.

Wannan saqone daga matasa masu san cigaban yankara da ke waye.

Stamped:
*Comr. Yusuf Lawal Abubakar*
*Comr. Anas Muhammad Sani Musa*
*Comr. Abberker A Tankor*
*Comr. Jamilu Usman Yankara*
*Comr Musa Sanusi*
08135559932

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here