Najeriya na Bukatar yiwa vangaren ilumin garambawul

0

Najeriya na Bukatar yiwa vangaren ilumin garambawul

Daga Zubairu Muhammad

An bukaci a yi ma harakar Ilimi garanbawul a Najeriya, matukar ba’ana so banagren ya durkushe gaba daya ba ne. kuma dole a samu Mutane kwararro a fannin dan ganin sun tsara yadda harkar ilimin zai tafi daidai da zama.

A kuma samar da kayan aikin da suka kamata. Mutukar ba’a daukin wannan mataki na gaggawa ba, to, lallai bangaren ilimi na gab da durkushewa.

Wannan kira dai ya fito ne daga bakin shugaban masu samar da bayanai na kasa da kasa a Majalisar dinkin Duniya wato Mista David Ukagu a lokacin da ake gudanar da wani taron tattaunawa dan nemu hanyoyin inganta ilimi a Najeriya a ranar Juma’ar da tagabata.

Taron wanda aka yi shi a cibiyar samar da bayanai na Malisar dinkin Duniya da ke Lagas ya tabo batutuwa da daman gaske. Mista Ukagun ya nuna matukar damuwar sa ta yadda akai ma Najeriya nisa a harkar Ilimi. Ya kara da cewa “yanzu a yanayin cigaban da aka samu a harkar ilimi a Duniya ya kai 4.1% amma a Najeriya ita har yanzu tana 1.7% ne,

kunga ko ai ba karamin nisa aka yi musu ba ko? musammamma a Arewacin Najeriya..”

David ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta bunkasa bangren ilimi wajen samar da kwararron Malamai, da samar da kayan karatu na zamani, sannan kuma a dinga ba malaman hakkokin su wanda ya kamata abasu.

Ita ma a nata jawabin babban mai kula da canjin yanayi (Climate Change) wanda bana Gwamnati ba, Mories Atoki, taba da shawarar cewa ya kamata a dinga koyar da karatu hade da sana’a saboda dalibai idan sun gama karatun su za su fito da sana’ar su, ta yadda ko basu sami aikin gwamnati ba za su iya dogaro da kanshi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here