0

Xan takarar Sanata ya raba littafan karatu a Qananan makarantun 5 a Nasarawa

Daga Zubairu Muhammad

Xan Majalisar wakilai ta tarayya dake wakiltar mazaber Doma da Awe da Keana Hon. Muhammad Agoshi Onawo ya rabawa dalubai a makarantun piramare dake wasu Qananan hukumomin Doma da Awe da Keana da Obi da Lafia lattatafan karatu a harshen Engilishi .
Anagabatar da shirin rabon lattatafan a makarantar L.E.A Akurba dake garin Lafia.

Da yake jawabi a madadin Xan Majalisar Shugaban yakin niman zavenshi Alhaji Dan juma Musa Garkuwan Daddare. Yace; a yankin mazaber Xan Majalisar wanan ba Sabon abu bane saboda ya saba yin makamancin irin wanan duk bayan wata uku yakanyi abubuwa dabam dabam domin taimakaon alumman mazabershi. Yace; a gareku mutanin qaramar hukumar Lafia da Obi wanan ya zama sabon abu gareku.
Ya kara da cewa Muhammad Ogoshi Onawo yana gabatar da shirye- shirye a mazaber shi domin taimakon alumma.
Baya ga Makarantu da makarantun koyon sana’a ga makarantar koyon kwamfuta ga kuma rijiyar burtsatse da yake ginawa a gurare dadama. Sannan yana biyawa yara tallafin karo ilumi wanan kuma ba sai a mazaber shiba harma a Lafia da Obi suna amfana da wanan tallafin sanan ya biyawa dubban dalubai kudin zana jarabawan WEC/NECO .
Xan Majalisar ya kai wutan lantarki gurare kusan takwas a mazabershi. Ga vangaren kiwon Lafiya saboda haka idan muka zave shi a matsayin Sanata muna zamu amfana da ire-iren cigaban da yake kawowa.
Ya kara da cewa wadanan litatafai da yawansu yakai 8250 Xan Majalisar yana da burin ganin yara sunyi karatu kamar yadda shima yayi saboda suma su zama kamarshi ko kuma su fishi.

Yace; yanzu babu abinda zakayiwa mutum ka birgeshi face ka bashi Ilumi . Idan ya samu ilumi yasan yadda zai gudanar da harkokin rayuwarsa.

Shima da yake Magana Shugaban makarantar Malam Agum Musa Muhammad yayi godiya ga Xan Majalisar saboda tallafin da yayi masu na Litattafai yace; Litattafai yana daya daga cikin abinda makaranta tafi bukata saboda idan zaka koyar da karatu babu Litafi yaran da kake koyar dasu bazasu fahinci abinda ake koyar da suba.
Amma tunda Allah yasa wanan bawan Allah ya waiwayemu ya kawo mana Littafi da za’arika koyar da dalubai mukuma zamu sanya ido moga cewa dalubai basuyi wasa da shi sun lalataba .
Shima da yake jawabi Shugaban PTA na makarantar Alhaji Ibrahim Muhammad yace; nidai xan Jami’iyyar APC ne kowa ya sani amma tsakani da Allah abinda wanan Xan Majalisar wakilai mai niman kujerar Sanata a mazaber Nasarawa ta Kudu yayi ya birgeni.
Saboda tunda muke garinnan babu wani xan siyasa mai mukami ko mara mukami da ya tabayi mana irin wanan abin cigaban.
Saboda haka yayi kira ga yan siyasa dasuyi koyi da abinda wanan Xan Majalisa Hon. Muhammad Ogoshi Onawo yakeyi . saboda taimakon alumma ne . idan kataimakawa yaro da ilumi ka daga darajan qasane saboda duk qasar da sukaci gaba sun cigabane ta hanyar ilumi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here