TURAKI YA YABA WA SANATOCIN DA SUKA CANZA SHEƘA

0

TURAKI YA YABA WA SANATOCIN DA SUKA CANZA SHEƘA

 Daga Bashir Suleman

Ya bayyana haka ne, a yau Talata,24/7/2018 ta hannun Daraktansa na harkokin sadarwa ta zamani da yaɗa labarai da kuma yakin neman zabe.

inda ya bayyana cewa ” Ɗantakarar Shugancin ƙasa a jam’iyyar PDP, Kabiru Tanimu Turaki ya yi lale marhabin da Ƴanmajalissar Ɗattawa na jam’iyya APC da suka canza sheƙa zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP, wanda hakan zai bai wa jam’iyyar PDP damar zama mai rijanye a majalissar.

Turaki ya ci gaba da cewa wannan ba ƙaramar nasara ba ce a siyasa dan haka yana ƙara yi masu maharbin da komowar Sanatocin jam’iyyar su ta asali.

Dan da haka ne, jam’iyyar tasu ta PDP za ta ƙara tsayuwa da jajircewa dan ganin ta ceto ƴan Najeriya daga cikin ƙangi da mayaudariya gwamnatin APC ta jefa su, na fatara da talauci da rashin tsaro da kashe kashen jama’a barkata da kuma matsin rayuwar da ke neman halaka ƴan ƙasar.

Haka kuma, Turaki ya maganta kan yadda jami’an tsaro suka ɓullo da salon takura wa Mutum na uku a gwamnatance a ƙasar nan, wato Shugaban Majalissar Dattawa Bukola Saraki da kuma Muƙaddashinsa Eke Ekweramadu, waɗanda jami’an tsaro suka tsare gidajensu ba bisa ƙa’ida ba. Wanda hakan zagon ƙasa ne ga siyasar ƙasar nan.

Sola Atete Daraktan yana labarai da kafafen sadarwa da kuma shirya yaƙin neman zaɓe na Ɗantakarar Shugabanci Ƙasa Kabiru Tanimu Turaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here