DA SANIN SHUGABA BUHARI: JAMI’AN TSORO SUKA TSARE GIDAN BUKOLA DA NA EKERAMADU

0

DA SANIN SHUGABA BUHARI: JAMI’AN TSORO SUKA TSARE GIDAN BUKOLA DA NA EKERAMADU

Daga Bishir Suleiman

Inji Kabiru Tanimu Turaki

A takardar da aka bai wa manema Labarai a ranar 22/7/2018, wadda Daraktan yaɗa labaru da tsara yaƙin neman zaɓen Alhaji Kabiru Tanumu Turaki, ya sanya wa hannu.

Ya bayyana cewa, Ɗantakarar Shugabacin ƙasar a jam’iyyar adawa ta PDP kuma tsohon Ministan ayyuka na musamman da ƙulla dangantaka a tsakanin ƙasa da ƙasa, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki, kuma Babban lauya a ƙasar nan (SAN) ya bayyana cewa babban mai kula da harkar tsaro a ƙasar wato Shugaba Buhari shi ne ya bai wa jam’ian tsaro damar tsare gidan shugaban majalissar dattawa Sanata Bukola Saraki da na mataimakinsa Eke Ekeramadu.

Turaki ya faɗi haka ne, a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke a Awka a taron ganawa da mambobin jam’iyyar da ke a faɗin ƙasar nan, don shirye – sheryen babban taron jam’iyya na ƙasa.

Ɗantakarar shugabancin ƙasar ya ƙara da cewa bai da shakku kan faɗar da sanin shugaban ƙasa Buhari, wajen takurar, don kawo karan tsaye kan cimma ƙudurin yarjejeniyar da suka ƙulla.

Jam’iyyar ta su ta PDP tsaye take ƙyam wajen yaƙar karan tsaye da ake wa Damokaraddiya a ƙasar nan.

Sun san cewar wannan canza sheƙa da Sanotoci da ƴanmajalissar wakilai suka yi daga jam’iyya mai ci ta APC zuwa PDP wata dama ce gare su ta mamaye zaurukan majalissun biyu, wadda ke nuna al’ummar ƙasar Najeriya za su gwaggwaɓi roman Damokaradiyya idan jam’iyyar PDP ta kafa gwamnati a 2019.

Ya tabbatar da ƙasashen da suka ci gaba na duniya, za su fahimci al’ummar ƙasar nan za su iya cire wa kansu kitse daga wuta.

Ɗantakarar ya tabbatar wa masu sauya sheƙar suna da cikakkar dama kamar kowa a jam’iyyar, su na da halarcin da za su iya taka rawa a kan takarar kujerun da suke so ba tare da wata tsangwama ba, dan dama gidansu ne, cirani suka je APC yanzu kuma sun dawo gida.

Turaki ya yi amfani da taron wajen zaburar da masu sauya sheƙar da basu tabbacin, cewar wannan dama ce da za su tallafawa juna, wajen sauya akalar tsarin gwamnatin tarayyar ƙasar nan, daga taɓarɓarewar da ya ke ciki a yanzu.

Ya tabbatar da rantsar da kwamitin da zai bayyana inda za a ƙara jaha, a yankin na Kudu maso Gabas, wadda da zaran sun samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa za su tabbatar.

Babban lauyan ya himmatu wajen samar da adalci da kwanciyar hankali, ya ƙara da cewa wannan gwamnati tare da majalissun ƙasar nan da masu ruwa da tsaki, su na amfani da shari’ah ne, don kare kawunansu ba su na amfani da ita ba, dan girmama doka.

Da suke magantawa Shugaban Jam’iyyar PDP na jahar Anambara Sir. Ndubisi Nwobuond da kuma tsohon kakakin majalissar dokoki ta jahar Emeka Anyaenetu sun yaba wa ɗantakarar Shugabancin ƙasar, sun kuma tabbatar masa suna da ƙwarin guiwar ya san matsalolin ƙasar nan da kuma yadda za a magance su.

Kazalika, da Ɗantakarar ya ziyarci Sakatariyar jam’iyyar PDP ta jahar Abia dan ci gaba da ganawa da mambobin jam’iyya, ya bayyana dawowar mambobin majalissun ƙasar guda biyu, ya nuna suna kan kyakkyawar aniya da za ta fitar da al’ummar ƙasar nan daga cikin ƙangin ƙaƙa-ni-ka-yin da rashin iya mulkin jam’iyya mai ci ta APC ta jefa su, na yawan kashe-kashe da fatara da zaman kashe wando.

Ya ƙara da cewa insha Allahu Allah za kawo wa al’ummar ƙasar nan sauyi, ta hanyar fitowar su don zaɓen da zai sauya wannnan gwambnati.

A nasa jawabin shugaban jam’iyyar adawar ta PDP na jahar, chif Johnson Onuigbo wanda aka fi sani da AKINBOARD ya bayyana cewar maganganun ɗantakarar abin burgewa ne da ƙara ƙarfin guiwa ga ƴan jam’iyyar, musamman da ya ke dogara da Ubangiji Allah a dukkan lamura.

Sola Atete
Daraktan ƴaɗa Labarai da tsara yaƙin neman zaɓe. Na Kabiru Tanimu Turaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here