TARON MASU RUWA DA TSAKI NA JIHAR KATSINA.

0

HAJJ 2018

TARON MASU RUWA DA TSAKI NA JIHAR KATSINA.

Daga Umar Cikingida

Yau Juma’a 27th July 2018 ne Amirul Hajj na bana Rt. Hon. Abubakar Yahaya Kusada, kuma Kakakin Majalisar. Dokokin Jihar Katsina, ya gudanar da taron masu ruwa da tsaki a kan aikin Hajjin bana.

Toron ya samu halartar duk hukumomin da kungiyoyin da jami’an tsaro da suka hada kai suna aiki tare domin ganin an yi aikin cikin nasara.

Hukimoni da suka halarci zaman sun haɗa da hukumar shige da fice ta ƙasa da Hana fasa ƙauri ta ƙasa, da hukumar hana sha fataucin miyagun ƙwayoyi da Jami’an Ƴansanda da jami’an tsaro na farin kaya da Sojojin sama da hukumar bayar da agajin gaggawa Ta ƙasa da sauransu.

Dukkan hukumomin sun bayyana wa Amirul Hajj cewa sun shirya tsaf domin ba da tasu gudumuwar.

Shima wakilin hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama, ya nemi da a basu haɗin kai don rage yawan mutanen da ke zuwa filin jirgi waɗanda basu da abunyi a wurin domin a bana za su yi amfani da terminal din domestic ba na international ba da aka saba.

Haka Shima wakilin CBN yace babban bankin ya shirya, ya tanadi wadatattun kuɗaɗen da za su ba wa mahajjata.

A nasa jawabin shugaban hukumar Alhazai ta jiha, ya bayyana cewa, hukumar ta tanaji duk abin da za a buƙata na tafiyar da aikin hajji na bana.

Haka zalika Shima Babban Jojin Jihar Katsina Maishara’a Musa Danladi Abubakar ya nemi duk hukumomin da su ba da haɗin kan da ake buɓata a garesu, domin a haɗa kai ayi aikin cikin nasara.

Daga Karshe shima Amirul Hajj, ya ƙara rokon dukkan hukumomin da ɓungiyoyin da su zo a ha kai ayi aiki cikin nasara, kuma yayi kira ga ‘yan jarida da su guji yada labarin da ba su da tushe, kuma koda ma labarin yanada tushe to a tuntubi dukkan bangarori domin samun daidaito.

Kuma ya gargaɗi ‘Yan social media da su guji yaɗa labaran kanzon kurege.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here