JAMI’AN KWASTAM SUN KAMA WATA KWANTAINA MAKARE DA KAYAN SOJOJI
Hukumar hana fasa kwauri ta kasa wato kwastam ta tsare wata kwantena da ke makare da kayan sojoji a kan hanyar Aba zuwa Fatakwal.
Joseph Atta, mai magana da yawun hukumar kwastam ya sanar da cewa jami’an hukumar dake Dhiyar C sune suka tare kwantenar ranar Juma’a.
“An dauki kwantenar ya zuwa Owerri inda aka gudanar da cikakken bincike a gaban wakilan mai kayan an samu dila 11 da dake dauke da dinkakkun kayan sojoji, ” Atta ya kara da cewa kowacce dila na dauke da setin kaya guda 400 dinkakku da kuma katon 15 na takalmin sojoji.
Tuni dai aka tsare wakilan mai kayan inda ake cigaba da gudanar da bincike.