Nelson Mandela ya koyar damu yadda zamu koyar da zaman Lafiya a duniya

0

Nelson Mandela ya koyar damu yadda zamu koyar da zaman Lafiya a duniya

Inji Sakataren MDD

Daga Zubairu Muhammad

A ranar Larabar da ta gabatane Nelson Mandela ya cika shekara Dari, a inda aka shirya gagarimin murna na taya wannan gwarzo cika karni daya. Babban bako mai jawabi a wurin taron shi ne babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya. Ga cikakken jawabin na sa da ya gabatar a wurin taron.
Ina matukar jin dadi da kasancewa tare daku a wajen wannan taya murna na rayuwar wannan bawan Allah mai amfani a wannan zamani na mu wato Nelson Mandela da ya ciki shekara Dari yau.

Na yi sa’ar haduwa da shi a rayuwata lokuta dabanm -dabam, ba zan manta da haduwar da na yi da shi na farko a Johannesburg ba,

tun kafin a zabe shi ya zama shugaban kasa. I lokacin na jinjina mai a kan wasu abubuwa kamar  yadda yake tsayuwa a kan ra’ayin sa, wayon sa, yadda yake tsara abubuwan sa, da kuma salon rayuwar sa.

Kuma ga shi a dalilin hakan yau ya farkar da mutane da yawa a kan neman ‘yancin su. Dan haka ya zama abun koyi ga Duniya baki daya yanzu, an koyii wasu abubuwa a wurin shi masu yawa kamar son zaman lafiya, son jama’a, aiki tukuru akan abu, iya mu’amala, girmama Mutane,aiki dan mutane su amfana, dama sauran abubuwa da daman gaske.

Mandela ya nuna mana wadannan abubuwan ba wai kawai da baki ba ne, ko kuma ya fada ya noke,  a’a ya aikata ne a aikace muka gani muka koya.

Ya ko ya mana yadda za mu tafiyar da rayuwar mu, yadda za mu girmama juna, yadda za mu zama masu yafiya, yadda za mu yi aiki tukuru dan Duniya ta sami salama da aminci.

Xan haka ko wace shekara a irin wannan  lokacin muke tunawa da kyawawan manufofin shi, musamman abun da ya shafi sadaukarwan shi da aiki tukuru.

A irin wannan sadaukarwanne saboda mutane su rayu ya jefa rayuwar shi cikin hatsari, ya hadu da makiya iri daban-dababn, aka sha kukkulle shi, amma duk da haka bai hakura ba, saboda ya san Allah ne ke kashewa da rayawa, ya ki yin saranda ko ya ja baya, ya ci gaba da fafutika har lokacin da ya sami ‘yanci shi da mutanen kasarsa,

mulkin farar hula ya kafu daram, har aka zabe shi ya zama shugaban kasa. Saboda haka dole ne ya zama Duniya tana tunawa da shi akan wannan namijin kokari da ya yi.

Xan haka wannan rana ta zama ranar Mandela (Mendela day) muna so Mutanen Duniya su sa wannan a kwakwalwarsu, kuma su yi ko yi da shi. Saboda shi Mandela ya fahimci cewa  mu ne za mu ta shi mu kirkiri abubuwa masu kyau a Duniya.  Duniya ta zama cewa ba nuna banbancin naunin fata, ba nuna banbancin bangarenci, ba nuna banbancin Addin da banbancin Jinci.
A samar ma da mutane aikin yi, Duniya ta musu dadi, kungiyoyi su san aikin su.
A takai ce dai yanzu wannan babban Mutum ya zama wani samfuri a Duniya na koyi da shi, dan haka muna kira ga al’ummar Duniya su ta shi haikan wajen koyi da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here