ZIYARARMU ZUWA KASAR RASHA

0

Daga Alhaji Hassan Dandy Kano 08032809899

Daular Tsar ta “yan Bolshevics

Ina zaune a gida bayan na dawo daga zagayen zumunchi na gaisuwar sallah aka kirani a waya ake fadamin Visa ta ta tafiya Russia ta fito, na cika da murna da farinciki saboda dalilai biyu, na farko nasan tsananin wahalar zuwa qasashen da ake kira Iron curtain na gabashin turai, wanda in banda arzikin kallon kowa na gasar Kwallon kafan Duniya lallai visar Russia akwai wahala sannan kuma ina cike da murna saboda ban san iyakacin littattafan da na karanta a matsayina na dalibin tarihi (history) zuwa novels da sauran documentaries akan Russia ba.

Mun tashi daga Airport ta Lagos muka hau Air maroc zuwa Casablanca, wanda daga nan ne kuma zamu hadu da sauran matafiya mu dauki hanya a abin da ake kira (transit)

A Casablanca mun yi kusan awa biyar na transit din kafin mu dauki hanya.

Bisa al’adata ko yaushe zan yi tafiya nakan zabi zama a Tagar jirgi ne (koda kuwa boarding pass dina bai nuna hakan ba nakan roqi wanda yake da kujerar tagar mu yi musanyen kujera) saboda tsawon tafiya nakan kalli screen na TV din jirgi in dinga calculating latitude, metres, degrees da maps har zuwa final destination, to kuma da yake dai a screen din duk za kaga birane da qasashen da ake ta wucewa still kuma zaka iya ka dinga leqawa ta tagar jirgin kana ganin garuruwan idan ma ba hazo ake ba har zaka iya sa’ar ganin dazuzzuka, rairayin hamada da tsaunuka, tituna gine-gine da sauran structures dai na birnin.

Mun fara da wuce Birnin Tangier na bakin tekun meditteranian na Maghrib, birnin karshe a nahiyar Africa. Ana wa Tangier lakabi da Birnin masoya saboda camfa birnin da akayi cewar in dai an kulla alkawarin aure a birnin to kuwa lallai mutu ka raba, ma’ana duk auren da aka kulla alkawarinsa a Tangier to kuwa auren baya mutuwa, wannan nema yasa daga ko’ina a duniya masoya samari da yammata ke tudadawa birnin in sun daidaita kansu domin wanzar da alkawarin, za ka ga yawanci ma samarin kan kyale zoben alkawari *engagement ring* har sai anje Tangier ne zai sanya a yatsan budurwarsa.

Ta tagar jirgi ina iya ganin Birnin Tangier da ragowar yamma a bakin tekun maliya. Tangier birnine da yake tsit ga tsabta ga furanni ko ina sannan kuma iskar tekun meditteranian din kan kwaso rairayin soyayya love sands cakude da dusar kankara tana bade fuskokin masoyan a bakin tekun.

Mun tsallaka gabashin Turai ta Meditteranian mun fara isa birnin Mallorca na yankin Andulus muka wuce Albacete har muka je helkwatar basque Valencia har ila yau na ga mashigar ruwannan ta Bilbao inda aka je karshen yakin nan na crusade wanda kiristocin Rum suka yanka milyoyin musulmi (Ance tun daga Cordoba zuwa Seville zuwa Bilbaon gawarwakin musulmi ne na lokacin iyakar ganinka) ina iya ganin mashigar Bilbao da aka ce saboda tsananin shekar da jinin musulmi da a ka yi a wajen, Balarabiyar Tangier da Rabat idan taje diban ruwa a bahar maliya tana iya gane jirkicewar ruwan zuwa kalar ja ja ja na jinin musulmi.

Mun wuce Qauyen Barcelonan Kataluniya shimfide kaman tabarma a bakin ruwa, har munyi tafiya mai nisa muna hango hasken fitilun garin.

Mun fita daga Spaniya muka ratsa Switzerland ta birnin Basel, kafin mu wuce ta saman Budapest din kasar Hungary

Mun ratsewa Kiev din Ukrainiya ta kudu muka bullowa Birnin Moscow a tsananin sanyi wajajan karfe 3 na dare, lokacin da muka zo Moscow Airports da ace rufe min ido akayi kawai na tsinci kaina a Moscow zan iya dauka birnin Dubai aka kaini, don tsarin Airport din escalators, lobby passages, lifters da rails duk irinsu daya da Dubai din, kai hatta na Arrival passages, taxi stands da ma titin da ya fita daga Airport din zuwa cikin gari duk iri daya suke

Dayake mun zo makare mun tarar jiragen saman da zasu kaimu Birnin Leningrad, St Petersburg( inda masaukin Super Eagles na Nigeria yake) daga Moscow duk bookings din ya cika saboda masu tudadawa Birnin, ala tilas muka tafi tashar jirgin kasa ta nan Moscow inda muka yi tafiyar kusan awa goma zuwa Leningrad din.

Abokan tafiyata yawanci basu ji dadin tafiya a jirgin kasar nan ba saboda gajiyar da muka debo tun daga Lagos, amma dai abinka da Explorer ni dadi ne ya kume ni na samu dama ta ganin Russian country side.

Wani abu da ya kara bani al’ajabi da saukar mu a Russia shi ne yanda instantly na fahimci duk da tsananin sanyi da suke ciki gaba dayan tsawon darensu Awa ukku ne rak, ma’ana zakaga karfe sha daya na dare a Agogo amma kuma rana bata fadi ba, sai sha dayan dare ake maghriba, kenan in abin mu yi gwari-gwari ne su suna Azimtar awa 21 ne a rana maimakon mu da muke azumtar awa 13 zuwa 14, kaman ace ne lokacinmu na buda baki zai koma 12 na dare, kaga kafin a gama sallar maghriba, isha’i da tarawih tuni alfijir ya keto babu maganar Sahur ma sam.

Insha Allahu a kashi na 2 da na 3 na rubutuna zan yi magana akan zamantakewar mutanen Russia, dangantakarsu da baki, tarihi da siyasarsu da kuma ziyarce ziyarce da na yi wurarensu na Tarihi.

Tare da abokina a jirgin kasa.
A bakin Otel a birnin Rasha
Tare da abokina cikin jirgi
Birnin Basalona daga sararin samaniya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here