Majalisar Dinkin Duniya zata taimakawa Nijeriya wajen yakan yan Ta’adda
Daga Zubairu T M Lawal Lafia
Masalisar dinkin Duniya da Gwamnatin Najeriya sun kulla yarjejeniya a tsakaninsu dan tunkarar fada da ‘yan Ta’addan Boko Haram da sauransu.Najeriyar dai ta nemi Masalisar din kin duniyar ne da su kawo musu agajin gaggawa dan ganin sun murkushe ‘yan kungiyar Boko Haram.
An dai kulla wannan yarjejeniyar ce a ranar Alhamis din da tagabata a babban birnin taraiya Abuja, a karkashin jagorancin Shugaban masu fada da ‘yan ta’adda na Majalisar dinkin Duniyar, wato Mista Vladimir Voronkov.
Sai kuma wacce zata taimakamasa a wannan aikin Mataimakkiyar Shugaban masu fada da ta’addanci na Majalisar din kin Duniyar wato Michele Coninsx.
Acikin tawagar da suka zo Abujan dai har da Babban Manajan tsare-tsaren lamuran Duniya a Masalisar dinkin Duniyar wato, Mista Alexander Avanessor. Sai kuma mai ba da shawara na musamman wajen kare aukuwar rikici a Duniya a Malisar dinkin Duniya.
Manufar zuwan wannan tawagar na Majalisar dinkin Duniyar Najeriya dai shi ne na yadda za su tattauna da gwamnatin Najeriya a gano ainufin wannan matsalar ta ‘yan Boko Haram. Sai kuma gano ainufin bangaren da Majalisar zata iya ba da gudun mawarta da kayan yakin zamanin xan taimakawa Najeriya wajen murkushe ko wane irin Yan ta’addanci.
Wakilan Majalisar Dinkin Duniyar dai sun sami ganawa da wasu jigajigan Jami’an gwmnatin Najeriya, ciki har da Mataimakin Shugaban qasa Farfesa Yemi Osinbajo, sai kuma manyan wasu Ministoci, da kuma Shugabannin wasu kungiyoyi, da wakilan kungiyar kare hakin Dan Adam, da Shugabannin Al’umma, da kuma Shugabannin kungiyoyin mata daban-daban.
Mista Voronkov ya shawarci Gwamnatin Najeriya akan su ba da goyon baya sosai akan wannan aiki da za’afuskanta na yaki da ta’addanci. Ya ce za mu yi iya kokarin mu wajen taimaka ma gwamnatin Najeriya akan wannan aikin, wanda zai zama aikin ya daidaita da na Duniya.
Gwamnatin Najeriyan ta nuna matukar jin dadi da wannan dauki da Majalisar dinkin Duniyar za ta kawo musu na yakar ‘yan Boko Haram din,kuma sun yi alkawarin ba da goyon baya akan aikin.
Gwamnatin ta ce za mu yi iya kokarin mu wajen baku goyon baya, da kuma ba sojoji goyon baya wadanda za su yi aikin, za kuma mu yi iya kokarin mu wajen ganin abun bai shafi farar hula ba musamman Mata da kananan yara.
Bayan kamala taron an kwashi tawagar Wakilan aka zagaya da su,Bulunkutu, da kuma tsakiyar garin Maiduguri, sun hadu da Kwamandar rundunar Sojoji da ke aiki a Maidugurin, sun kuma gana da wasu kungiyoyi daban-daban, kuma sun ziyarci wurin da ake ba yara Maza da Mata horo, dan dawo musu da kyakykyawar rayuwar su.
Kuma har iya yau sun ziyarci babban filin tashin jirgin sama dake Abuja, a inda suka yi maganar cewa da bukatuwar a kara inganta filin tashin Jirgin saman da na’orori na zamani.
Akarshe dai an tattauna wasu hanyo da ake ganin su ne za su kawo karshen wannan rikici na Boko Haram wanda yaki ci –yaki cinyewa, hanyoyin dai sun hada, da wani tsari wanda majalisar dinkin Duniya suka yadda da shi wajen yaki da ta’addanci, wanda kuma shi ake amfani da shi a Duniya baki daya.
Za’abi wasu hanyoyi domin dakume faruwar rikici tun kafin ya abku. Da kuma tabbatar da amba kowa hakin sa . inganta hakin Mata da kananan Yara. Inganta harkar tsaro a fannin Jirgin Sama da na Kasa. Da kuma sa ido sosai akan kan iyakokin qasashe. Sai kuma amfani da jawaban sirri.