Gwamnan Akwa Ibom, da Turaki sun ƙalubalanci Rikicin Jahar Benue.
Sun bayyana haka ne, a wata ziyara da Ɗantakarar shugabanci Ƙasar ya kai a jahar Akwai Ibom.
A takardar da Daraktan yaɗa labaran ɗantakarar ya rabawa manema labaru. Ta nuna gwamnan Udom Emmanuel da Turaki sun soki yadda rikicin ke daƙile cigaban siyasa a jahar ta Benue.
Sun faɗi haka ne, a wata ziyara da Ɗantakarar shugabacin ƙasar, ya kai a gidan Gwamnatin Jahar da ke Uyo, a ranar litinin tare da tawagarsa a cigaba da ziyarar da suke kai wa dan ganawa da jiga jigan jam’iyyar. Inda suka samu tarba daga Gwamnan jahar da kakakin majalissar da sauran mambobin majalissar da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
Gwamna Emmanuel ya bayyana yawaitar tashe tashen hankula da ake fama da shi, a jahar Benue da babban abin takaici, wanda hakan ba ƙaramar gazawa ba ce a shugabancin ƙasar.
A nasa jawabin Turaki ya ce Damakaradiya a ƙasar Najeriya na cikin mawuyacin hali, da ya haifar da rashin haɗin ka da kwanciyar hankalin jama’ar ƙasar. Ba ƙaramar damuwa, ya jefa mafi yawancin jama’a ba.
Ya kuma gargaɗi jama’a da ka da su kuskura, su sake kuskuren zaɓen gwamnatin APC a karo na biyu, saboda kurakuran da ta tafka na gaza kare rayukan al’umma, wanda ya yi sanadiyar wargaza cigaban su, duba da yadda hakan ya tarwatsa cigaban siyasa da tattalin arziki a jahar Benue.
Turaki ya zargi gwamnatin APC da rashin iya mulki, wanda ya janyo fatara da talauci da rashin tsaro, amma duk da haka jam’iyyar su ta PDP ta gwada ita gwana ce a jahar Akwa Ibom wajen iya mulki da kyautatawa jama’ar jahar ta hanya kyakyawan jagoranci da amfani da ilmi da natsuwa da sanin ya kamata.
Wanda hakan halaye ne fitattu na jam’iyyar PDP, don haka nake shawartarku a wajen zaɓen fitar da gwani a mataki na ƙasa, duk da dai jam’iyyar tamu tana da zaƙaƙuran ƴantakarar shugabancin ƙasar nan, amma ku zaɓe ni dan nafi kowa siffantuwa da waɗannan kyawawan ɗabi’u.
Ina mai alƙawarta maku zamu tsara yadda za a magance matsalar tsaron da ake fama da shi a ƙasar nan, da ta tattalin arziki data galbaitar da al’umma.
Haka kuma, muna alƙawarta maku za mu fito da wani fasali da zai yi bita kan yadda aka bayar da shawarwari kan tsare tsaren da aka tattauna a taron ƙasa da aka gudanar a shekarar 2014.
A nasa jawabin Gwamna Udom ya bayyana Turaki a matsayin babban Mutum wanda yasan tarin ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta da yadda za a magance ɗumbin matsalolin.
Gwamnan ya ƙara da cewa jam’iyyar tasu tana da zaƙaƙuran ƴantakara a matakin shugabancin ƙasar nan, kamar yadda ta nuna, gwamnoni su na ta ɓullowa a cikin jam’iyyar kuma suna da cikakken tabbacin za a yi kowa adalci a wajen zaɓen fitar da gwani.
Haka kuma, Turaki shi ne mutum na farko da ya kawo masu irin wannan ziyara a sakatariyar jam’iyyar dake Uyo dan ganawa da masu ruwa da tsaki da masu kuri’u a wajen zaɓen fitar da gwani ta ƙasa.
Shi ma shugaban jam’iyyar PDP na jahar Obong Paul Expo ya yabawa Turaki da ƴan tawagarsa, da yadda suke ƙara ɗinke barka dake a cikin jam’iyyar.
Sole Atere,
Daraktan Yaɗa labarai da kafar sadarwa ta zamani da kuma tsare yakin neman zaɓen Ɗantakarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP Kabiru Tanimu Turaki SAN