Alia Ghaniem itace Mahaifiyar usama ibn Ladan shaharrren Dan gwagwarmayar nan Dan asalin Saudiyya
Wanda ya yaki sojan rasha ya kuma kwama da Amurka..daga baya sojan Amurka suka kashe shi a kasar fakistan
A hirar ta ta farko da wata Jaridar burtaniya. Tace Dan usama mutumin kirki ne..kuma ya na kaunarta Yana kuma kyautata mata.yana mata da a da biyayya.
Tace tayi Masa horo da tarbiyya Mai kyau…Amma a Jami a. Ya hadu..da wasu da suka juya Masa kwalwa da tunani suka mai da shi Mai tsaurin ra ayi..
Tace ganinta na karshe da usama shine a 1999 da suka je Inda yake a kasar .. Afghanistan..
Tace Bata ji dadin abinda da ake cewa danta yayi…kuma tayi bakincin rasuwar sa…