BUHARI/MASARI CONSULTATIVE FORUM.

0

BUHARI/MASARI CONSULTATIVE FORUM.
_________________________________
Kungiya Mai suna a sama kalkashin jagorancin Tsohon kakakin majalisar dokoki ta jihar katsina Hon.Yau Umar Gwajo, Gwajo Garkuwan Daura, Turakin Damagaram.

Takai ziyara ta’aziyya ga Dan takara kujerar Sanata na zaben cike gurbin yankin Daura Hon. Ahmad Babba Kaita kan hadari da wasu na cikin tawagar yakin Neman zaben shi sukayi jiya juma’a Wanda yayi sanadiyar rasuwar mutum daya wasu da dama suka samu raunuka.

Bayan gama ta’aziyyar tareda yin addu’a ga wanda rasu da wadanda suka samu raunuka. Allah ya jikan Wanda ya rasu yaba wadanda suka samu rauni lafiya. kungiyar ta mika ma Dan takarar Sanatan gudumuwa ta kayan campaign, kayakin sun hada da.

(1) Banners, guda Dari (100)
(2) T-shirts, guda Dari biyar(500)
(3) Posters, guda dubu ashirin(20,000).

Gudumuwar kungiyar bata tsaya kan bada kayan campaign kadai ba, daga gobe idan Allah ya kaimu kungiyar zata cigaba da bin lungu da sako na yankin Daura baki daya Neman Alfarmar Al’ummar yankin Daura kan su zabi Dan takara APC Hon. Ahmad Babba Kaita na Buhari.

Dan takarar sanatan Hon. Ahmad Babba Kaita ya nuna jin dadin shi da godiyar shi ga shugannin kungiyar kan wannan gudumuwa da suka kawo mashi.

Daga cikin shugabannin kungiyar na jiha da suka samu damar zuwa ta’aziyyar tareda shugaban kungiyar Akwai, Dr. Bashir Gambo Saulawa, Hon. Musa Adamu Funtua, Hon. Bala Sani Yaya Ingawa, Hon. Bilyaminu M. Rimi.

Sign By. Surajo Yandaki

Katsina State APC Social Media Crew.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here