MANYAN YAN FIM DAGA KUDUNCIN NIJERIYA MATA DA SUKA AMSHI MUSULUNCI
meye dalilansu na fita daga Kiristanci?
Hotunansu da bayanai
Daga Danjuma Katsina.
1.Moji Olaiya mahaifinta shahararren mawakin ne ta yi aure har sau biyu ta na shan wahala, a kan haka ta hadu da wani musulmi yana mata bayanin yadda za ta samu kwanciyar hankali tabi shawararsa, sai taga ta samu natsuwa.
Ai sai kawai ta musulunta, ta kuma auri musulmi
2.Vivian Metchie ubanta mabiyin Katolika uwarta kuma ta na bin Difa life, sai tace Kiristanci ya cika rudu sai ta fara bincike a kan musulunci sai ta musulunta.
3. Lizda Silva binciken kashin kai a kan musulunci ya sanya ta musulunta ta bar Kiristanci
4. Lizzy Anjorin matsalolin rayuwa ya sa ta musulunta ta tafi aikin Ummara a kasa mai tsarki. don neman mafita
Kuma tana dawowa komai na rayuwar ya canza sai ta zama yar gani kashe ni musulunci
5. Laide Bakare mijinta kirista ya rika azabtar da ita ta kai kuka cocinsu aka kasa warware mata halin da ta shiga sai ta fice da Kiristanci ta shiga Musulunci ta auri musulmi kuma rayuwarta ta canza.
6. Lola Alao muhawara ta rika yi da wani malamin musulunci a facebook, suka it muhawara sai ta gamsu da hujjojinsa sai ta Musulunta