Shugaba Buhari ne zai samu Nasara a zaben 2019 in ji Wamako.

0
780

Shugaba Buhari ne zai samu Nasara a zaben 2019 in ji Wamako.

Daga Bishir Suleiman

A wata takarda da mataimaki na musamman kan harkokin kafar sadarwa ta zamani da yaɗa labarai Bishir Rabe Mani ya sanya wa hannu, ta bayyana shugaban ƙungiyar sanatocin yankin Arewa, Sanata Aliyu Wamakko ya ce a rubuta a aje, shugaba Buhari ne zai sake samun nasara a babban zaɓe mai zuwa na 2019.

Ya faɗi haka a gidansa dake Gawon Nama Sokoto a gaban sama da mutane miliyan guda, magoya bayan jam’iyyar dake sassa daban dabam na jahar sokoto a ranar asabar.

A lokacin da ɗumbin magoya bayan Sanata Wamakko, dake a faɗi jahar suka tarbe shi tare da yi masa lale marhabin da dawowa daga babban birnin tarayyar Abuja.

Wamakko dake wakiltar Sokoto ta Arewa a majalissar dattawa ya bayar tabbacin har yanzu jahar Sokoto tana hanun jam’iyyar APC, mutanan jahar kuma suna goyan bayan tafiyar Shugaba Buhari.

Ya kuma yi kira ga ƴan majalissarsu na Apc da su ƙara haɗa kansu, su kawar da duk wasu maganganu da ake kan shugaba Buhari bai yi wani cikakken aiki ba a jahar.

Ya ce Shugaba Buhari a shirye ya ke da karɓar dukkan ingantaccen aiki da aka tukare shi da shi wanda zai amfani al’ummar jahar ta fuskar shan roman damokaradiya.

Sanatan ya ƙara da cewa jam’iyyar su ta Apc ita ce wadda ta samu nasara a jahar dama ƙasa baki ɗaya, dan haka, yake ƙara kira ga ɗumbin magoya bayan jam’iyyar da su ƙara riƙeta hannu biyu biyu.

Da yake magantawa kan sauya sheƙar da gwamnan Tambuwal ya jagoranta, zuwa PDP, ya ce shi babu wata taraliya tsakanin sa da gwamnan, sai da tsakanin jam’iyyarsa ta APC da kuma PDP.

Sai dai tausaya wa masu sauya sheƙar zuwa PDP, ganin yadda jam’iyyar ta PDP ta riga ta gama mutuwa.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban jam’iyyar na jahar Alhaji Isa Sadiq Acida ya ce har yanzu al’ummar jahar, suna goyan bayan tafiyar Shugaba Buhari da Sanata Wamakko.

Ya cigaba da cewa shakaru takwas tsakanin 2007 zuwa 2015 da Wamakko ya yi a matsayin gwamnan jahar sokoto, ya kawo cigaba matuƙa wajen bunƙasa tattalin arziki a jahar.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, sanata Ibrahim Abdullahi Gobir, ya ce a mamadinsa da sauran ƴanmalissa bakwa daga cikin ƴanmalissu sha ɗaya dake wakiltar jahar a majalissar dokoki ta ƙasa suna bayan Shugaba Buhari da Wamakko saboda gaskiya da dattakonsu.

Haka ma, ɗaya daga cikin ƴanmajalissun, Alhaji Musa S. Adar, ya tabbatar shugaba Buhari ba zai bar jahar sokoto, baya ba, wajen aniyarsa ta bunƙasa ƙasar Najeriya.

A nasa jawabin a mamadin ƴanmajalissar dokoki ta jahar, su sha biyu da suka tsaya a cikin jam’iyyar ta APC, Sani Alhaji Yakubu da ya fito daga mazabar Gudu ya bayyana cewa wakillai sha takwas na zauren majalissar sun sauya sheƙa zuwa PDP amma suna ƙoƙarin sake haɗewa da jam’iyyar ta APC.

Tsahon kawamishi nan tsaftace muhalli na jahar Alhaji Muhammadu Bello Sifawa ya ce ba zai manta da namijin ƙoƙari da sanata Wamakko ya yi ba, wajen kawo cigaba a lokacin da ya ke gwamnan jahar, wanda shi shaida dan a lokacin yana cikin zauren majalissar gudanarwa ta jahar.

A nasa jawabin tsohon sakataren gwamnatin jahar Alhaji Bello Muhammadu Maigari Dungyaɗi ya ce shugaba Buhari a lokacin yakin neman zaɓensa ya alƙawarta zai farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa da magance matsalar tsaro da kuma yaki da cin yanci da rashawa wanda kuma duk ya tabo su a gwamnatinsa.

Ɗantakarar gwamna a jam’iyyar APC a jahar wanda kuma ya kasance tsohon kwamishi nan kuɗi a gwamnatin baya, Alhaji Faruk Malami Yabo ya ce har yanzu jama’a suna goyan bayan tafiyar APC kuma a shirye suke da su ƙara zaɓar shugaba Buhari a zaɓen 2019 mai zuwa.

Taron ya samu hartar manyan baki da suka haɗa Jakadan Najeriya a Tanzania Ambasada Sahabi Isa Gada da kuma tsohon Jakadan Najeriya a Marocco, Ambasada Shehu Wurno da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here