Amirul Hajji na Jahar Katsina ya yi Bankwana da ƴan jigin Farko.
Daga Bishir Suleiman
Amirul Hajj na jaha kuma Kakakin Majalissar dokoki ta jahar Katsina, Rt. Hon. Abubakar Yahaiya Kusada, ya yi matuƙar farin ciki da godiya ga Allah da kawo mu lokacin da mahajan jahar katsina za su fara tashi, sannan ya yi gargaɗi ga mahajan da su kiyaye doka da oda ta yadda za su ƙara ƙasar nan da jahar katsina kwarjini a idon duniya.
Jirgin ya ɗebi mahajatan da sula fito daga yankunan Ɗandume, Faskari da Bakori da Ɗanja wanda tun aka gama tantace su da basu ƙuɗaɗen su na guzari.
Haka kuma a ɓangaren hukumar Alhazai suna ta ƙara wayar da kan mahajatan kan su guji tafiya da duk wani abu da doka ta hana tafiya da shi da kuma kira da su kula da ƙuɗaɗen guzurin su sosai dan gudun salwanta.
Jirgin ya tashi wajajen ƙarfe 3:25 na daren lahadi 6/8/2018 a farfajiyar tashin jirage ta ƙasa da ƙasa ta Umaru Musa Ƴar’adua dake a jahar Katsina.
Kuma tuni hukumar Alhaza ta cigaba da tantance masu tafiya a jirgin na biyu wanda ya ƙunshe mutanan Sabua da Futua da sauransu.