KUDUDDUFIN GANDUJE
Daga Kabiru Yusuf Fagge Anka
Duk lokacin da hadari ya taso, har zuwa lokacin da ake fara ruwa hankulan al’ummun da ke wajen da masu bin hanyar a tashe suke saboda sun tabbatar kududdufin (wanda aka yi a matsayin gadar kasa) zai cika da ruwa, ba mamaki ya ci gidajensu ko ya ci mutum, sannan masu bi ta hanyar don zuwa garuruwa da unguwanninsu sai dai su hakura da bi ta hanyar.
Kai a karshe dai wannan kududdufi sai da ya ci mutum. Wannan aikin gadar kasa da sama da Ganduje ya yi a hanyar Dorayi da Panshekara da Madobi ya tabbatar mana da irin aika-aikar da Ganduje ya sha fada, ashe shi yake tafkawa.
Duk lokacin da aka yi ruwa sai gadar ta cika ta batse, har ta haifar da abubuwan da na fada a sama. Wannan ya nuna rashin iya aiki imma daga aika-aikar gwamnatin ko na dan kwangilar wanda ake kyautata zaton shi ya yi aiki ne ta abin da ake cewa “yadda aka dama haka za a sha,” kamar yadda gwamnan ya sha fada.
Ba zan iya yin shiru ba sai na yi kira ga mai girma gwamnan jihar Kano Ganduje don Allah a yiwa al’ummar Kano bayanin irin damarwar da aka yi a wannan gada, kuma a gyarata kar kududdufin ya cinye unguwannin da ke kusa ko ya ci gaba da cinye mutane.
Idan kuma ba za a gyara ba, to don Allah a ciketa a yi kwalta, abin da aka ci Allah ya gani, idan ya so wani gwamnan idan ya zo a 2019 idan ana bukata ya yi ingantacciya, ni dai shawara ce tawa, Allah ya sa ka yi aiki da abin da na fada.