KARIMCIN KUNGIYAR YANKASUWA GA ALH DAHIRU MANGAL (GOC NA ALHERI).
Kyautar karramawa da kungiyar ‘Yankasuwa ta kasa tai wa fitaccen Dankasuwa kuma Babban Dansiyasa Dan Asalin Jihar Katsina a Ranar 07/07/2018, a Dakin Taro na hukumar kula da kananan hukumomi da ke Katsina ya zaburas da Kasidarmu ta Idon Makwarwa ya aza Dankasuwar bisa Sikeli, don tabbatar da Cancantar Wannan Karimci ga Alh Dahiru Mangal.
Binciken Idon Makwarwa ya jiwo ra’ayin Mutane 60 daga sassan Nigeria Wanda ya tabbatar da Alh Dahiru Mangal a matsayin mafi girman fada a ji a harkar kasuwanci da Siyasa a Jihar Katsina.
Haka kuma Sakamakon Binciken ya tabbatar da Alh Dahiru Mangal a matsayin Dankasuwa kuma Dansiyasa mafi kima daga Jihar Katsina.
Daga cikin Manyan Dalilan da suka ba Alh Dahiru yin carar da ake ji ko ina har da kasancewarsa wanda ya fi Samawa mutanen Katsina aiyuka a kamfanoninsa da dama.
Haka kuma Shine mafi girma cikin masu taimakon Yankasuwa da Jari. A nasu 6angaren Yansiyasa na kiransa GOC saboda yawan Alherinsa, da basira wajen Harkar Siyasa, saboda ba Yansiyasa da Shugabanni Mafita kan matsaloli.
Tarihi ya tabbatar da cewa a Shekarar 2005 ne aikin Hajji a Nigeria ya shiga halin Ni ‘Ya su, saboda gazawar kamfanonin Jiragen Nigeria kai Alhazzai Hajji. A Wannan lokaci ne Zuciyar Katsinawa ta Kumburowa Alhaji Dahiru Mangal inda ya lashi takobi ga Gwamnan Wannan lokaci Marigayi Umaru Musa Yaradua cewa Katsina ba ta kara Jin kunya kan aikin Hajji. Nan take ya kafa kamfanoninsa na Max Air, kuma da Shekara ta gewayo aka fara kwasar Alhazzai daga Katsina.
A yau, duk Nigeria babu kamfani irin Max Air. Max Air na jigilar Hajji ga kasashen Duniya da dama.
Domin kara kwarjini da hucewa yan Nigeria haushi, max air na jigilar cikin Nigeria. Dukkan Jiragen Max Air Sabbi ne da suka cika ka’idojin Kasa da kasa.
Ta fuskar kyauyatawa Al’umma kuma, kasidar Idon Makwarwa ya yi fira da Limamai da Malaman Addini sama da 100, kuma Sakamakon firarrakin ya nuna gagarumar gudumuwar da Alh Dahiru Mangal ke bayarwa wajen Gina Masallatan Juma’a da na Hamsussalawati da Makarantun Addini.
A ta bakin wani malami mai Almajirai, Shirinsa na ciyarda marasa galihu da Almajirai da marasa lafiya da ake kullum, da kuma sadaka ga Almajirai na rage radadin talauci cikin Al’umma.
Shi kuwa Mal Kabir Ali, mazaunin Birnin Katsina, cewa ya yi, abu mafi ban Sha’awa da ya bambanta Alhaji Dahiru da Sauran Tajirai shine yadda ya dage ga Tarbiyya da baiwa ‘Ya’yansa Tarbiyya da Ilimi mai zurfi kuma bai barsu suka rena mutane ba.
Binciken Idon Makwarwa ya tabbatar da cewa Alhaji Dahiru ne Bakatsine mafi fada a ji a fagagen Kasuwanci da Siyasa a ciki da wajen Jihar Katsina, kuma ana sauraren murya da Umarninsa a kasashen Duniya da Dama. Ke nan, kungiyar ‘Yankasuwar Nigeria ta yi Karimci inda ya dace.
Allah sa Alheri, Amin.
Alh Salisu Sada Ruma
Danwairen Katsina ya rubuta