HAJJIN BANA
DAGA Cikingida
Ƙimanin mutane dubu ɗaya da dari shidda da sittin da ukku (1663) daga Jihar Ƙatsina sun sauƙa a birnin Madina lafiya.
Jirgi na farko da ya tashi a ranar Lahadi 5/8/2018 ya dauki maniyyata 556 da suƙa fito daga ƙanan hukumonin Bakori, Danja, Dandume, Faskari,Funtua, Sabuwa. Jirgi na biyu wanɗa ya tashi ranar litinin 6/8/2018 ya ɗauki maniyyata 546 da suka fito daga kanan hukumonin Funtua, Batsari,Safana, Danmusa, Dutsinma da Ingawa.
Shikuma jirgi na ukku wanda ya tashi jiya Talata 7/8/2018, ya ɗau maniyyata 561 da suka fito daga ƙanan hukumomin Kankia, Kusada, Musawa, Matazu, Daura, Mani da wani ɓangare na maniyyata daga karamar hukumar Malumfashi
Ya zuwa yanzu babu wata matsalar da ta taso ma alhazan mu duna ciki ƙoshin lafiya suna kuma gida nar da ayyukan su na zuyara a birnin Manzo SAW watau madina.
A cikin kowane Jirgi da ya tashi ya kan haɗa da jami’an lafiya don gudun ko takwana su bada agajin gaggawa a cikin girgi.
fatan mu dai shine Allah ya sa ayi wannan aiki agama cikin nasara kamar yadda aka fara shi cikin nasara.