MARS THREATENS US WITH THE FORCE OF WAR

0

MARS THREATENS US WITH THE FORCE OF WAR

Mars closest to Earth on July 30-31

Shekaru wajejan 463 da suka gabata Nostradamus a cikin Littafin sa na Hasashe yayi hasashen baiyanar Tauraruwar Duniyar Mars ta yanda kowa zai iya ganinta. Hasashen baiyanar ita tauraruwar ta Mars yazo dadai da wajejan da shi Nostradamus yake magana akan yaƙin duniya na uku da kuma Wani Bawan Allah zai baiyana, wankan tarwaɗa daga Iraƙ. Kamar yanda masu fassara suka fassara. Suna nufin Imam Mahdi(A) ne.

A ranar 27/07/2018 watau ranar da akayi Khusufin wata duk wanda ya kalli lokacin da khusufin yake fatuwa zai ga daga gefe bangaren dama, daga inda wata yake akwai wata tauraruwa mai haske kamar yanayin na watan a lokacin watau kalar haskenta yayi ja. Ga wadanda suke da application mai labarta yanayin sararin sama irin su *Sky Safari5* ko *Night Sky* da makamantan nau’ukansu zai iya bibiyar yanayin sararin sama sosai.

Nostradamus ya baiyana cewa ganin wannan tauraruwar zai sabbaba Yaki da zai sheƙar da jinin kashi saba’in (70%) a cikin dari. Wannan maganar tasa kamar ya ɗaukota daga zantukan hadissan Ahlulbaiti (A). Domin Imam Sadiƙ ya gaya ma wani daga sahabbansa cewa kafin tabbatar wannnan lamarin na Imam Mahdi(A) sai an share biyu bisa ku. Sai mutumin ya kiɗime sai Imam Sadiƙ(A) yake cewa da shi ashe baka fatan ka zama cikin ɗayan da zai ragu? Wasu ruwayoyin sunzo da cewa kaso biyar cikin bakwai. wasu kuma kaso Tara cikin goma. Allah ne masani.

Irin wannan baiyanar da ita wannan tauraruwar ta Mars da tayi, da irin wannan sigar bai aukuba tun bayan rubuta littafin na Hasashen lamuran ƙarshen zamani na Nostradamus. Sai a wannan shekarar ta 2018.

Duk da cewa manazarta a wannan zaman da suke magana ko ince tsokaci akan yaƙin duniya na uku wasunsu sun nuna cewa da yiwuwar kaso ɗaya bisa uku ne za a iya rasawa. Har wasu na ganin cewa a yankin Asiya zuwa Afrika da yiwuwar za a iya rasa mutum miliyan 200 zuwa Miliyan 300. Allah ne masani.

Amma a yankin Amerika kuwa sun ƙiyasta cewa da yiwuwar za a iya rasa mutum wajen Miliyan 700 ne. Bansan ko da wannan dalilin bane su Amerikawan suka duƙufa wajen wayarwa da jama’arsu kai. Dangane da haɗarin da yake fuskantosu ba? Ga wanda ya kalli film din da suka gabayar mai suna *Deep Infact* zai ga haka. Ga kuma littafai da suka wallafa irinsu *Alive after the Fall* , ga kuma *Survival Mindset Keeping Calm Assertive after the fall*, da kuma *Secrets To sanitization After the Fall*. Da makamantan irinsu.

Malaman Bible sun gaya mana dangane da Amerika a lokacin faɗuwarta. Ya zo a cikin Wahayin da akayiwa Yahaya(Revelation) Babi na 16:19-21. Ya ɗan labartayanda lamarin na rushewar Amerika da yanda zai kasance kamar haka:

19 Babban birnin nan kuwa ya rabu gida uku, biranen al’ummai kuma suka fāɗi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, don ya sa ta, ta sha fushinsa mai tsananin gaske. 20 Kowane tsibiri ya ɓace, manyan duwatsu ma ba a ƙara ganinsu ba. 21 Waɗansu manyan ƙanƙara kuma kamar kayan jaki suka faɗo a kan mutane daga sama, har mutane suka zagi Allah, saboda bala’in ƙanƙarar. Bala’in nan da matuƙar bantsoro yake!

Sannan a Babi na 18 ananma an labarta mana kamar haka:

8 Saboda haka, bala’inta zai aukar mata rana ɗaya, Mutuwa, da baƙin ciki, da yunwa. Za a kuma ƙone ta, Domin Ubangiji Allah da yake hukunta ta, shi Mai Ƙarfi ne.”

*9 Sarakunan duniya kuma da suka yi fasikanci da zaman almubazzaranci da ita, za su yi mata kuka da kururuwa, in sun ga hayaƙin ƙunarta,*

*10 za su tsaya a can nesa, don tsoron azabarta, su ce, “Kaitonka! Kaitonka, ya kai babban birni! Ya kai birni mai ƙarfi, Babila! A sa’a ɗaya hukuncinka ya auko.”*

*11 Attajiran duniya kuma suna yi mata kuka suna baƙin ciki, tun da yake, ba mai ƙara sayen kayansu.*

Littafin Bible ya gaya mana cewa “Masu alamun sujada a goshinsu zasu tsira” wanda wannan kamar yana yi mana nuni da cewa; kamar lamarin ba zai shafi ƙasashen musulmai ba sosai. Allah ne masani.

Ga cikakken abinda Nostradamus yace akan wannan lokacin na baiyanar Tauraruwar ta duniyar Mars. Da zata baiyana ta yanda kowa zai iya ganinta. Za a ci gaba da ganinta tun daga July, 2018 har zuwa September na 2018.

*Mars threatens us with the force of war, and wil couse blood to be seventy times.The clergy will be both exalted and reviled moreover, by those who wish to learn nothing of them.*

Wannan fahimta tace ba lallai bane ya zamana haka abin yake, ko kuma ince haka shi Nostradamus yake nufi ba.

Allah ka tsare bayinka Albarkacin Ma’asumai.(A) Ka jarabta mu gwargwadon abinda imaninmu zai iya ɗauka. ka sanya ƙarshenu ya kasace Shahada a ƙarƙashin tutar zaɓaɓɓen bawanka Almasihu(A) mai ceto a ƙarshen zamani

Ya Allah ka gaskata mana maganganun bawanka Muslih dangane da kasarmu Nijeriya. Ka kasance tare dashi a inda yake. Ka cikanmasu burinsu na ganin bayan azzaluman mahukuntan asarmu Nigeriya.

Muhammad Sani Ra’is, Funtua.
+2347034595991
22111439
04082018

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here