Yaƙin Neman Zaɓen Cika Gurbi ya Tara jigajiga Jam’iyyar APC

0

Yaƙin Neman Zaɓen Cika Gurbi ya Tara jigajiga Jam’iyyar APC

A safiyar yau Alhamis ne, filin jirgin sama na Malam Umaru Musa Ƴar’adua dake jahar Katsina, ya cika da jirage ɗauke da jiga jigan jam’iyyar APC da suka zo dan gudanar gaggarumin gangamin yakin neman zaɓen Ahmad Babba Kaita.

Jirgin farko ya sauka ne wajajen karfi sha ɗaya dauke da Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, da sanata dake wakiltar shiryar Funtua da Katsina ta tsakiya da wasu sanatoci biyu daga jahar kano.

Yayin da jirgi na biyu ya kawo Ministan Sufarin jiragen sama, da wasu daga ciki masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta APC

See also  HADUWATA DA JELANI ALIYU 

Inda jirgi na uku ya sauka da misalin ƙarfe 11:03, ɗauke da muƙaddashin shugaban ƙasa Professor Yami Osibanjo, wanda ya samu rakiyar gwamnan jahar Kano Dr Abdullahi Ganduje.

Tawagar Muƙaddashin shugaban ƙasar ta samu tarba daga gwamnan jahar katsina Rt Hon Aminu Bello Masari da Kakakin Majalissar dokoki ta jahar Katsina da kuma Shugaban Ma’aikatan Gidan gwamnati Alhaji Bello Mandiyya da saura jama’a

Bayan sun gama gaisawa da jama’a, wasu daga cikin tawagar Gwamnan jahar Katsina su kai bai wa muƙaddashin shugaban kyautar ƙwarya.

Daga nan kuma suka ɗunguma suka tafi Daura inda za a gudanar taron yakin neman zaɓen maye gurbin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here