Jam’iyyar APC ta Tsarota da Haɗin kan da Babbar jam’iyyar Adawa ta PDP ke Samu, inji Turaki.

0

Jam’iyyar APC ta Tsarota da Haɗin kan da Babbar jam’iyyar Adawa ta PDP ke Samu, inji Turaki.

 

daga Bishir Sulaimin

A takarda da aka raba wa manema labarai, ɗantakarar Shugabanci ƙasa a jam’iyyar adawa ta PDP kuma tsohon Minista kan ayyuka na musamman da kuma ƙula hulɗa tsakanin ƙasa da ƙasa, Kabiru Tanimu Turaki SAN.

Ya ce ” jam’iyyar APC dake riƙe da madafun iko, ta faɗa ciki tsoro da fargaba wanda zai haifar da durƙushewarta, sakamakon matsalolin san zuciya na ƴan jam’iyyar.

Da kuma lura da ƙarin haɗin kan da jam’iyyar adawa ta PDP ke samu, tun kafin su kai ga ƙwace gwamnati da hannun APC

Ya cigaba da cewa, za su rasa gwamnati, saboda ƴan Najeriya sun gaji da soya masu aya a hannu da jam’iyyar APC ke masu, dan haka za su cirewa kansu, kitse daga wuta, ta hanyar amfani da katunan zaɓe, su kori gwamnati maci wadda a kullum take masu roman baka, alhali suna cikin fatara da yunwa da rashin aikin yi da rashin tsaro da zaman kashe wando da yawan tashe tashen hankulan da cin amana da yi wa doka karan tsaye.

Ɗantakar Shugabacin ƙasar ya bayyana haka ne a sakatariyar jam’iyyar PDP, da ke a Akure ta jahar Ondo a ranar labara, a cigaba da ziyarar da suke yi dan ganawa da masu ruwa da tsaki na PDP, game da batun babban taron jam’iyyar na ƙasa da za aɓta gudanar nan gaba.

Ɗantakarar ya kuma ƙalubalanci yadda jam’iyyar APC ke nuna tsauri tare da bambanci wajen yakar cin hanci da rashawa, ya ƙara da cewa ya lura an fi ƙarfafa kai hari ga waɗanda suka kafa jam’iyyar ta PDP tun Shekarar 1999.

Ya cigaba da cewa, idan an duba addadin wanda ke cikin APC a yanzu, masu riƙe da muƙamai da kuma wanda suka sauya sheƙa zuwa cikinta. Za a fahimci ba ƙanana mahandama ke cikinta ba, waɗanda suka gwanance wajen cin hanci da rashawa, amma kuma su ne ake wa kallon tsarkakku abin girmamawa ga hukumar kula da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati.

Amma da zarar wani mai riƙe da madafun iko, ya sauya sheƙa zuwa PDP sai a ci gaba da ƙalubantarsa da ci mutuncinsa da yaɗa shi a kafafen sadarwa na zamani.

Ya kuma bayyana cewa, cin hanci bai tsaya ga satar kuɗin al’umma ba kawai, har ma ya yi tambaya me yasa APC take rashin adalci wajen samar da ayyuka kuma me yasa ake nuna bambanci a tsakanin jama’a, kawai dan ba a fito jaha ɗaya ba, ko kuma dan ba a zaɓi APC, to, shi wannan me ne ne?

Haka kuma, ya ƙalubalanci yadda gwamnatin ta lalata tattalin arzikin ƙasar nan, wanda ta gada a ranar 29/5/2015 wanda shi ne mafi matuƙar cigaba a ƙasashen nahiyar Afirika, kuma na uku a duniya baki ɗaya, baya ga ƙasar China da Qatar, ƙwararru suka tsara kuma suka ɗora ƙasar nan, kan shi domin cin gajiyar shi a tsawon lokaci.

Turaki ya ce da zarar kwamitin sun tsayar da shi takarar shugabanci ƙasa, cikin sauki za su warware matsalar rashin tsaro da ta adabi yankin arewa maso gabas, zarar an ba shi dama, ya samu nasarar arewa kan mulki zai zamo tarihi.

Kazalika, ya ce ba su bari a raba ƙasar nan ba, za su yi bakin ƙoƙarin ganin ta zamo duƙulalliya, ta hanyar zamowa al’umma, gadar da za gina ƙasar nan, da kuma fitar da mutane daga halin ƙangin da aka jefa su.

Dan halin da ƙasar nan ke ciki, ba ƙarami bane, sai mun haɗa kai tare da tsayuwar daka dan warware halin da aka jefa ta ciki.

Ya kuma yi kira ga shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa Uche Secondus, da ya fito da kyakkyawan tsari na gaskiya da amana wanda kowa zai yadda da shi, ya kuma daidaita sahun ƴan jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here