Samada Mutane 5000 sunyi hijira zuwa PDP a Nasarawa
Daga Zubairu Muhammad
A makon dayagabatane duban ya’yan Jami’iyyar APC mai mulki sukayi hijira daga Jami’iyyar tasu zuwa Jami’iyyar adawa ta PDP.
Akasarin yan hijirar suna sanyene da jajayen huluna wanda ya nuna ya’yan kungiyarnace ta Kwankwasiyya mazansu da mata inda suka mamaye harabar Sakatariyar PDP dake garin Lafia.
Dubban mutanin sun cigaba da rera wakokin PDP na yaboga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Dayake jawabi babban bakon da ya wakilci Sanata Kwankwaso. Architect Aminu Dabo yace yayi farin ciki da yaga dubban Nagoya bayan Sanata Kwankwaso cikin Jihar Nasarawa, ya kara da cewa magoya bayan Kwankwaso mutanine masu akidar gaskiya saboda suna kaunar Sanatanne ba saboda yana basu kudiba sai xan yana aikinda yadace tare da kwantan yanchin talaka a duk inda yake a qasan nan .
Architect Dabo yace; muna sauya sheka daga Jami’iyyar APC mai mulki ne , badan komai ba saidan rashin adalci da rashin kaunar alumma. Ya kjara da cewa; Babu abinda tsalakawa suka amfana dashi a Gwamnatin Buhari ta APC, kuma kokabada shawara ga yadda za’ayi ba’a sauraran shawarar mutani ,ana mulkin kama karya. Yace; zasu kara shiga lungu lungu da sako a jihohi duk inda magaya bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suke duk zasu sauya sheka su dawo PDP. Ya kara da cewa ; Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kamar yadda akayi zave a 2015 yazo na biyu a zaven fidda gwani a APC yabaiwa Buhari goyon baya saboda akafa Gwamnati mai tausayi amma aka kasa tausayawa talakawa wanan babban daliline da zai sanya alumma su guji APC. Yakama yi kira ga duk membobin Jami’iyyar da alumma kowa ya amshi katin zave.
Shima a nasa jawabin Shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Fransis Orugu, ya bada tabbacin cewa za’a ba wadanda suka sauya sheka dama a jam’iyyar da kuma karfafa su donmin ansan rijistan Jami’iyyar t PDP a koina cikin qananan hukumomi.Jihar.
Yakara da cewa dama PDP gidane ga yan qasa illa iyaka wasu am bata masu raine shiyasa suka bar gidajensu sukaje wani gida to amma yanzu an gyara gidan saboda haka babu damuwa idan mutum ya dawo gidansu na gado tunada Kwankwaso da sauran su psuna da haqi a PDP kuma gidansune munyi murna da dawowansu. Ya jara da cewa yanzu Amana da Power sun hade waje daya alamun nasara ta tabbata ga PDP a qasa baki daya.