WASU MA’AURATA DA SUKE SAYAR DA ‘YA’YANSU SUN SHIGA HANNUN HUKUMA.

0

WASU MA’AURATA DA SUKE SAYAR DA ‘YA’YANSU SUN SHIGA HANNUN HUKUMA.

Duniya, ina za ki da mu? Jami’an ‘yansandan jahar Imo sun yi nasarar cafke wasu mats da miji waɗanda ake tuhuma da laifin sayar da yara, a ciki ma har da ‘ya’yansu.

Ugochuku Nwachuku da matarsa Victoria Nwachuku sun amsa laifinsu ba tare da sun wahalar da hukuma ba.
A lokacin da kwamishinan ‘yansandan jahar ta imo Mista Dazuki Galadanci yake tuhumarsu a shalkwatar ‘yansandan jahar, Gloria ta bayyana cewa sun sayar da yaran a kan farashin Naira dubu ɗari shidda (600,000). Amma ta ce baban abinda ya ba ta takaici shi ne lokacin da mijinta ta sayar da ɗansu na fari lokacin yana wata huɗu kacal da haihuwa. Kuma ya ninke kuɗaɗensa ba tare da ya ba ta ko sisi ba.

See also  YAN BINDIGA SUN KAI HARI A KANKIA

Shi kuma Ugochukwu ya musanta batun nata inda ya ce; “na yi nufin shiga makarantar koyon aikin soja ne, kuma ga shi ba ni da kuɗaɗen da zan biya makarantar. sai na shaewarci matata kuma ta amince muka sayar da ɗanmu a kan Naira 400,000. A ciki na sayi babur kuma na fara sana’ar kiwon kifi. Daga nan muka ci gaba, sai a wannan na karshen ne asirinmu ya tonu”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here