AHMAD MUSA YA SAMU TARBA TA KARRAMAWA A KASAR SAUDIYYA.

0

AHMAD MUSA YA SAMU TARBA TA KARRAMAWA A KASAR SAUDIYYA.

A yau ne fitaccen ɗan kwallon Najeriya Ahmad Musa ya sauka a filin jirgin sama na Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya. Ya samu kyakkyawar tarba daga ‘yan sabon kulob ɗin da ya koma mai suna Al-Nassr.

Dan kwallo Ahmad Musa shi ne ɗan kwallo ma fi kwazo na takwas a wasan cin kofin Duniya 2018 da aka gudanar kwanaki a kasar Rasha. Kuma ya yi canjin sheka ne daga Leicester city.

A lokacin saukar tasa dandazon masoyans sun zo ɗauke da tutocin sabon kulob ɗin nasa suna masa marhabin lale.
Kulob ɗin ya bayyana cewa Ahmad ya sanya hannu a kan kwantiragin shekaru huɗu a kulob ɗin. Sai dai ba su bayyana ainahin nawa kulob ɗin ya biya shi ba da ya shigo. Amma dai wasu rahotanni sun bayyana cewa, an ba shi Uro miliyan 25 ne.

See also  THE DUALIZATION OF THE KANO - KATSINA ROAD IS AT ITS PEAK!

Ahmad wanda yake cike da farin ciki da wannan tarba, ya watsa hotunan nasa a shafinsa na sada zumunta a yanar gizo. Inda ya yi godiya ga karramawar da aka yi masa, ya kuma gode wa dukkan wani wanda ya zo don tarbarsa. Ya kara da cewa, ya ji matukar daɗi da wannan dama da kulob ɗin Al-Nassr ya ba shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here