AN LADABTAR DA DIREBAN HAYIS SABODA CIN ZARAFIN WATA MATA DA TA SA HIJAB DA NIKAB.
Wani kamfanin hayar motoci samfurin hayis dake kasar UK ya ba da hakuri a kan kyarar wata mai nikab da wani direban hayis ya yi lokacin da za ta hau motarsa. Wannan mace wacce ta yi shigar musulunci ta zo hawa motar tare da ‘yarta mai shekaru biyu don ta je Birnin Bristol daga Easton. Ta yi matukar mamaki a lokacin da direban fafur ya ce ba za ta shiga ba sai ta cire nikab ɗin dake fuskarta.
Wata mace wacce ke sanye da hijabi ita ma ta yi farat! Ta mai da martani ga direban inda ta ce, “na rasa dalilin da zai sa ka damu da shigar da ta yi, domin jikinta ne, kuma za ta iya yin dukkan shigar da ta ga dama”. Shi kuma direban ya mai da mata martanin cewa, ” dole ne na damu mana domin Duniyar ta zama abin tsoro, sai an fi samun kwnciyar hankali idan ana kallon fuskokin juna”.
A yayin zantawarsa da ‘yan jarida a kan yadda ya kyamaci wannan mace kamar wata ‘yar ta’adda. Direban ya ce, tsoro ne ya kama shi. Gani yake kamar za ta shigo motar ne don ta sa musu bam.
Matar ta bayyana cewa, babban abinda ya ɓata mata rai shi ne, yadda bayan ya barta ta shiga motar, a hanya ya ci gaba mitar cewa watakila ta shigo musu da bam.
Matar ta ce, ta yi matukar kunyata a cikin jama’a kan abinda ya faru. A yanzu haka dai kamfanin hayar motocin ya ɗauki matakin ƙladabtarwa ga wannan direba mai wuce makaɗi da rawa. Sun ce kamfaninsu ba ya kyamatar dukkan mutane daga kowacce kasa, kowanne addini ko kuma kowanne launin fata.