KATSINA VOCATIONAL CENTRE: SAMARWA MATASA MAFITA SHI NE BURINMU

0

KATSINA VOCATIONAL CENTRE: SAMARWA MATASA MAFITA SHI NE BURINMU

In ji Alhaji Salisu mai kamfanin Continantal Computer, a yau lahadi 12/8/2018 a ɗakin taro na Sakatariyar jahar Katsina, wajen gaggarumin biki yaye ɗalibai na cibiyar horas da matasa karo na sha biyar.

Taron ya samu halartar Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Sanusi Lamiɗo Sanusi na II da Cigarin Katsina da kuma Ƙauran Katsina wanda ya samu wakilcin Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, da sauran Hakima da magaddai.

Haka kuma taron ya samu halartar Babban Jojin Jahar Katsina Maishari’ah Musa Ɗanladi Abubakar da Alƙalin Alƙalai Alhaji Abdulhafiz da sauran masu ruwa da tsaki da dama daga ciki da wajen jahar Katsina.

Taro ne wanda cibiyar ta saba aiwatar tun bayan da aka assasa ta a shekara ta 2000 ƙarƙashin jagorancin Alhaji MD Yusuf wanda Allah ya yi wa rasuwa a shekarar 2015, a ɗabi’ar cibiyar tana yaye ɗalibai a duk shekara, tana kuwa horas da matasa sana’o’i da dama tare da basu kyauttuka na kayayyakin sana’o’in da suka koya dan su je su dogara da kansu.

Kamar yadda ɗaya daga cikin ƴan majalissar gudanarwa cibiyar ya bayyana, kayyakin da ake rabawa ga waɗanda aka horas ɗin ana samar da su ne daga tallafin da ake samarwa dan gudanar da cibiyar.

Haka ma, Alhaji Salisu Kaɗanɗani shugaban kamfanin Continantal Computer, ya yi tanbihi game da jawabin mai martaba Sarkin Kano dangane da adadin yaran da basa samun ko da ilmin Firamare, wanda illar ta fi shafar yankin Arewacin ƙasar nan, inda ya yi kira da kowane mutum wanda ke da Almajiri mai masa hidima a gidansa da ya taimaka ya sanya shi a makaranta boko.

See also  FG says 2nd Niger bridge ready by Xmas

Kazalika, ya yi kira ga jama’ah da su ƙara himmatuwa wajen gina rayuwar matasa da tallafawa ƙoƙarin gwamnati dan ciyar da ilmi a gaba. Ya kuma koka ƙwarai game da halin da Matasa suke ciki wanda ya ƙuduri aniyar tallafa masu a kowane mataki daga cikin abin da Allah ya hore masa.

A nasa jawabin godiya, Alhaji Aminu MD Yusuf ɗa ga wanda ya assasa cibiyar ya yi godiya ƙwarai ga maharta taron da kuma yi masu fatan alheri da addu’ar Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya.

Shugaban cibiyar Malam Ɗanjuma Katsina ne, ya amshi takardun shaidar gamawar ɗaliban daga hannun mai Martaba Sarkin Kano dan rabawa ga ɗaliban sannan kuma aka ci gaba da bayar da kyaututuka ga ɗalibai.

Waɗanda suke ta godiya da sambarka da addu’ar Allah ya jiƙan wanda assasa cibiyar ya kuma saka wa shugaban cibiyar da masu tallafa mata da alheri.

Daga bisani Ratibin babban limamin Masarautar Katsina, Liman Malam Ɗayyabu ya rufe taro da addu’ah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here